Sabuwar qidaya: Yawan masu amfani da yanar gizo a kasar nan ya kai ya kawo

Sabuwar qidaya: Yawan masu amfani da yanar gizo a kasar nan ya kai ya kawo

- Masu amani da yanar gizo sun kai 100m da doriya

- An samar da layukan ne a zamanin mulkin PDP

- Yanzu kam kwalliya ta biya kudin sabulu

Sabuwar qidaya: Yawan masu amfani da yanar gizo a kasar nan ya kai ya kawo
Sabuwar qidaya: Yawan masu amfani da yanar gizo a kasar nan ya kai ya kawo
Asali: Original

A shafinta ta yanar gizo, inda take bayada rahotannin wata-wata kan yadda masu samar da layukan sadarwar yanar gizo ke habaka, hukumar NCC mai kula da ka'idojin harkar sadarwa, tace an sami qarin mutum miliyan dake amfani da layukan intanet a fadin kasar nan.

Rahoton, ya shafin watan Agusta ne kawai, inda aka kwatantashi da watan Yuli na bana, inda ya nuna mutum kusan 950,000 ne suka karu kan layukan sadarwar zamani ta intanet din.

A watan Yuli dai, masu amfani da yanargizo 103.5m ne, amma a yanzu sun haura 104.6 million, wanda ke nuna habaka aka samu ba takurewa ba.

DUBA WANNAN: Rikici a Jos ya hallaka 14

Kasar NAjeriya dai na da jama'a kusan 190m, wanda ke nuna akalla rabinsu na samun hanyar samun bayanai na zamani.

Sai dai in aka yi la'akari da wadanda ke ajje layuka biyu, da masu aiki na sana'a, za'a sami cewa ba lallai 100m din duk mutum daya yake nuufi ba.

Kamfanin AIrtel mai arahar data ita ta fi kowacce cikin kishiyointa samun karin kwastomomi da kusan 450,000, sai MTN inda ya biyo baya da 380,000, sannan Glo da 250,000, inda ita kuwa 9mobile, samun raguwar kwastomomi tayi da layuka 120,000.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel