Matatar mai ta dangote ta karbi kayan aiki na musamman don fara aiki
- A Legas ake aikin gina matatar man ta Dangote
- Zata fi kowacce girma a nahiyar Afirka
- Zata fara aiki ne a badi in sha'a kaddara

Asali: UGC
Wani katafaren jirgin ruwa daga kasashen Yammacin duniya ya iso Ikko bakin teku don fara sauke wasu muhimman kayan ayyuka da ake bukata a matatar mai ta Dangote, wadda ake sa rai zata hau aiki gadan-gadan a badi.
Matatar, wadda ke jihar Legas, zata fara tace mai wanda ake sa rai NAjeriya da makwabta zasu mora, zata fi kowacce kafasiti a nahiyar Afirka.
Jirgin ruwan, na kamfanin BB Chartering, ya kwaso kayan aikin ne daga Dubai, da ma Afirka ta kudu.
DUBA WANNAN: Matatun mai sun fado warwas
Dangote dai yace yaci bashin akalla dala biliyan hudu da rabi, don a samu a kammala matatar a kan kari.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng