Manyan mutane 4 da suka sa labule da Buhari a taron majalisar dinkin duniya (Hotuna)

Manyan mutane 4 da suka sa labule da Buhari a taron majalisar dinkin duniya (Hotuna)

A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kasar Amurka domin halartar taron koli na majalisar dinkin Duniya karo na 73 dake gudana birnin New York, ya samu zantaawa da wasu gagga gaggan shuwagabannin kasashen Duniya.

Legit.ng ta ruwaito Buhari yayi wannan ganawarce da shuwagabannin bayan sun sanya labule inda suka goga gemu da gemi kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi bukatun junansu.

KU KARANTA: Yajin aiki: Zamu hana jiragen sama sauka da tashi daga Najeriya – Kungiyar kwadago

Manyan mutane 4 da suka sa labule da Buhari a taron majalisar dinkin duniya (Hotuna)
Buhari da shugaban kasar da na Afirka ta kudu
Asali: UGC

Daga cikin wadanda shugaba Buhari ya gana da su akwai shugaban kasar Ghana, Nana Akufo Addo, wanda suka tattauna dashi game da barazanar da jama’an kasar Ghana ke yi ma yan kasuwan Najeriya mazauna Ghana.

A yayin ganawarsa da shugaban na Ghana, Buhari ya gayyaci ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama da mashawarcinsa akan al’amuran tsaro Babagana Monguno son su bada gudunmuwarsu a yayin tattaunawar.

Haka zalika Buhari ya goga gemu da gemu da shugaban kungiyar kasashen musulmai a duniya, OIC, Dakta Yousef Ahmed Al-Othaimeen, sai kuma shugaban majalisar dinkin duniyar kanta, Antonio Gutteres.

Manyan mutane 4 da suka sa labule da Buhari a taron majalisar dinkin duniya (Hotuna)
Buhari da shugaban UN dana OIC
Asali: UGC

Daga karshe shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tattaunawar sirri da shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, shima anan sun tattauna batutuwan da suka shafi matsalar nuna wariya da jam’an kasar Afirka ta kudu ke nuna ma sauran yan Afirka da kuma hanyoyin hada kai game da matsalar tsaro.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng