Mataimakin gwamna ya karyata barin APC, yace yana nan daram dam

Mataimakin gwamna ya karyata barin APC, yace yana nan daram dam

- Mataimakin gwamnan jihar Oyo ya karyata jita jitan ya koma ADC

- Ya Kwatanta zancen da gutsuri tsomar marasa cigaban jihar

- Duk da dai ya ajiye burin takarar kujerar gwamnan jihar, amma har yau yana APC

Mataimakin gwamna ya karyata barin APC, yace yana nan daram dam
Mataimakin gwamna ya karyata barin APC, yace yana nan daram dam
Asali: UGC

Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Moses Adeyemo ya karyata jita jitar cewa ya koma jam'iyyar ADC.

Kamar yanda yake a jawabin mataimakin shi na musamman, Mista Sola Adegoke, Adeyemo ya Kwatanta hakan da gutsuri tsomar marasa son ganin cigaban jihar.

Duk da dai ya tabbatar da cewa ya ajiye burin takarar kujerar gwamnan jihar, amma har yau yana nan daram a jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Yadda aka sha yajin aiki a Najeriya a yau

"Ina nan daram a jam'iyyar APC a jihar Oyo. Inason cigaba ni a rayuwata kuma nayi aiki tukuru wurin ganin kafuwar jam'iyyar a jihar."

"Duk da dai na ajiye burin takarar kujerar gwamnan jihar, ina nan a jam'iyyar. Nayi kuma mamakin inda jita jitar ta bullo. Wadanda ke yada jita jitar su bayyana shaidar cewa na koma ADC kawai. Wannan aikin marasa son ganin nasarar jam'iyyar APC ne a jihar Oyo." inji Adeyemo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel