New York: Uwar gidan shugaban kasa Buhari ta gabatar jawabi a taron yaki da cutar tarin fuka

New York: Uwar gidan shugaban kasa Buhari ta gabatar jawabi a taron yaki da cutar tarin fuka

- Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, ta gabatar da jawabi a taron da ake tattaunawa kan yaki da cutar tarin fuka

- Taron wanda ya ke gudana a birnin New York, ya samu halartar kusan shuwagabanni ko wakilansu daga kasashen duniya

- A wani labarin kuwa an saki hadimin uwar Aisha Buhari, da ta zarga da yin awo gaban da kudinta da suka kai akalla N2.5bn

Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Muhammdu Buhari, ta gabatar da jawabi a wani babban taro da ake tattauna hanyoyin da za a yaki cutar tarin fuka TB don kawo karshenta a fadin duniya. Taron na daga cikin jerin tarurrukan babban taron kasa da kasa karo na 73 #UNGA wanda majalisar dinkin duniya ta shirya.

Taron wanda ya ke gudana a birnin New York, ya samu halartar kusan shuwagabanni ko wakilansu daga kasashen duniya, wanda ake tattauna muhimman batutuwa da suka shafi kasar da kuma samar da hanyoyin inganta kyakkyawar alaka tsakanin kasashen da majalisar dinkin duniya UN.

Aisha Buhari, ta shiga sahun takwarorinta na kasashen duniya wajen kawo hanyiyin da za a dakile yaduwar cutar tarin fuka, musamman a wannan lokaci da cutar ke yaduwa a cikin al'umma tare da yi masu kisan kwaf daya.

New York: Uwar gidan shugaban kasa Buhari ta gabatar jawabi a taron yaki da cutar tarin fuka
New York: Uwar gidan shugaban kasa Buhari ta gabatar jawabi a taron yaki da cutar tarin fuka
Asali: Twitter

A wani labarin:

Hukumar tsaro ta fararen kaya SSS, ta saki hadimin uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, da uwar gidan shugaban kasar ta zarga da yin awo gaban da kudinta da suka kai akalla N2.5bn da ya karba daga hannun 'yan siyasa da ke bata a matsayin kyauta tsawon shekaru 3 ba tare da ya bata ko kwabo ba.

KARANTA WANNAN: An gurfanar da wani mutumi a gaban kotu bisa zarginsa da sayar da zinaren bogi akan N500,000

Yayan Mr Baba-Inna, Farouq Baba-Inna ne ya sanar da cewa hukumar tsaro ta SSS ta sallami kanin nasa bayan da hukumar ta gaza gano wadannan makudan kudade ko sama ko kasa a wajen hadimin uwar gidan shugaban kasar.

A baya NAIJ .com ta ruwaito maku cewa uwar gidan shugaban kasar, Aisha, ta karyata rahotannin da ke cewa ita ce ta bada umurnin cafke hadiminta, tana mai jaddada cewa jami'an tsaro ne suka gudanar da aikinsu a kanshi.

New York: Uwar gidan shugaban kasa Buhari ta gabatar jawabi a taron yaki da cutar tarin fuka
New York: Uwar gidan shugaban kasa Buhari ta gabatar jawabi a taron yaki da cutar tarin fuka
Asali: Twitter

KARANTA WANNAN: Anambra zata samu filin jirage na kasa da kasa idan har na zama shugaban kasa - Atiku

Ta karyata rahoton ne ta a cikin wata sanarwa daga hannun daraktan watsa labaranta, Suleiman Haruna, a ranar Talata, 25 ga watan Satumba. Sai dai ta bayyana dalilin danya sa aka kama hadimin nata, tana mai cewa tsawon shekaru 3 yana mata aiki, tare da karbar kudaden da 'yan siyasa suke bata a matsayin kyauta, da suka kai akalla N2.5bn wanda bai taba bata ko kwabo a ciki ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel