Kudu-maso-Yamma za ta koma hannun PDP idan na zama Shugaban kasa - Atiku

Kudu-maso-Yamma za ta koma hannun PDP idan na zama Shugaban kasa - Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya sha alwashin ganin Kudu maso Yammacin Najeriya ta koma hannun Jam’iyyar PDP idan har aka zabe sa a matsayin Shugaban kasa a 2019.

Kudu-maso-Yamma za ta koma hannun PDP idan na zama Shugaban kasa - Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya nemi goyon bayan yarbawa
Asali: Depositphotos

Atiku wanda yana cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar ta PDP mai adawa yace Kudu-maso-Yammacin Najeriya za ta koma karkashin PDP idan har aka zave sa ya zama Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019.

Atiku Abubakar ya bayana wannan ne lokacin da ya gana da manyan PDP a Garin Ibadan da ke cikin Jihar Oyo inda yake neman su mara masa baya a zaben fitar da gwani da za ayi kwanan nan domin fitar da ‘Dan takarar PDP na 2019.

KU KARANTA: Ambode ya shiryawa zaben fitar da gwani a APC

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya tunawa jama’a yadda su ka karbe Kasar Yarbawa daga Jam’iyyar AD a 2003. A wancan lokaci dai Legas ce kurum ta gagari Gwamnatin Obasanjo tabawa lokacin Bola Tinubu yana Gwamnan Jihar.

Alhaji Atiku yace Yankin na kasar Yarbawa za su ga canji idan PDP ta hau mulki inda yake sa ran shi ne zai zama Shugaban kasar. Atiku ya shiga Ibadan ne tare da tsohon Gwamna Otunba Gbenga Daniel wanda shi ne Darektan yakin neman zaben sa.

‘Dan takarar Shugaban kasar ya nemi mutanen Jihar Oyo su marawa Jam’iyyar su ta PDP baya a zabe mai zuwa Atiku yace Jihar ta Oyo ita ce Hedikwatar siyasar Kasar Yarbawa baki daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel