Guguwar canji: Tsohon gwamnan Bauchi, Yuguda, ya tsallaka zuwa APC

Guguwar canji: Tsohon gwamnan Bauchi, Yuguda, ya tsallaka zuwa APC

Mallam Isa Yuguda, tsohon gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam'iyyar PDP ya canja sheka daga jam'iyyar GPN zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Shugaban jam'iyyar GPN a jihar Bauchi, Alhaji Sani Mohammed Bura, ne ya tabbatar da hakan yayin wata ganawa da jaridar Daily Post.

Ya bayyana cewar Yuguda ya koma jam'iyyar APC ne domin cigaba da gwagwarmayar siyasa.

"Ina mai tabbatar maku cewar tsohon gwamna Yuguda ya koma APC. Duk da magoya bayansa dake GPN sun bi shi zuwa APC, mutane iri na sun cigaba da zama a jam'iyyar domin ko a yanzu da nake magana da ku ta wayar tarho ina kan hanyar zuwa jihar Enugu domin halartar wani taro na jam'iyyar mu ta GPN," a cewar Bura.

Idan baku manta ba, Yuguda na cikin tsofin gwamnonin PDP da hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ke sansana domin ko a 'yan kwanakin nan saida hukumar ta garkame wani gidansa.

Guguwar canji: Tsohon gwamnan Bauchi, Yuguda, ya tsallaka zuwa APC
Isa Yuguda
Asali: Depositphotos

Mohammed Abubakar, gwamnan jihar Bauchi da ya gaji Yuguda ya ci alwashin bin dukkan hanyoyi da doka ta amincewa domin karbo duk wata kadara ko kudi da gwamnatin da ta gabace shi tayi sama da fadi da su.

Bura, ya bayyana cewar Yuguda ya sanar da magoya bayansa batun canjin shekarsa daga GPN zuwa APC.

A jihar Oyo kuwa ‘yan majalisar dokoki 9 sun canja sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta ADC. Daga cikin mambobin da suka fita daga APC din har da mataimakin shugaban majalisar, Honarabul Abdulwasi Musah.

DUBA WANNAN: 2019: Wata kungiya ta je yiwa Buhari kamfen a majalisar dinkin duniya

Magatakardar majalisar dokokin jihar Oyo, Paul Bankole, ne ya karanta wasikar canjin ‘yan majalisar yayin zamansu nay au, Talata. Bayan mataimakin shugaban majalisar, daga cikin wadanda suka canja shekar akwai, Lukman Balogun, Bolaji Badmus, Azeez Billiaminu, Ganiyu Oseni, Olusegun Olaleye, Samson Oguntade da Muideen Olagunju.

Yanzu haka jam’iyyar ADC na da mambobi 12 a majalisar ta jihar Oyo yayin da jam’iyyar APC dake mulkin jihar keda mambobi 18. Jam’iyyar PDP na da mambobi 2 kacal a majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel