APC ta yiwa Dogara wankin Babban Bargo a jihar Bauchi

APC ta yiwa Dogara wankin Babban Bargo a jihar Bauchi

Jam'iyyar APC reshen jihar Bauchi, ta yiwa shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, wankin babban bargo dangane da yadda ya yi amfani da ita tamkar wani tsani domin cimma burikansa da ta misalta lamarin a matsayin cin moriyar Ganga da ya da koron ta.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, jam'iyyar ta fedewa Dogara Biri har wutsiya da cewar tsintacciyar Mage ba ta Mage sakamakon yadda ya juyawa jam'iyyar baya a yayin da ya gama cin moriya karkashin inuwar ta.

Babban mai bayar da shawarwari kan harkokin shari'a ga jam'iyyar, Rabi'u Abubakar, shine ya yiwa Dogara wankin babban Bargo a madadin jam'iyyar yayin da ganawarsa da manema labarai a jihar ta Bauchi.

APC ta yiwa Dogara wankin Babban Bargo a jihar Bauchi
APC ta yiwa Dogara wankin Babban Bargo a jihar Bauchi
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 20 ga watan Satumbar da ta gabata ne shugaban majalisar ta wakilai ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar ta PDP inda ya bayar da dalilinsa na cewa, ba bu wani abu da jam'iyyar APC ta tsinanawa jihar Bauchi cikin dukkanin alkawurran da ta daukarwa al'ummar Najeriya.

KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta bayyana dalilin kame Dogarin ta

A yayin ci gaba da bayyana fushinsa, Mista Rabi'u ya kuma musanta zargin Dogara kan cewa gwamnatin jam'iyyar APC ta yi hobbasa iyaka bakin kokarin ta a bangaren tattalin arziki, tsaro, noma da kuma yakar cin hanci da rashawa cikin shekaru ukun da suka gabata.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta cafke Sani Baban-Inna, babban Dogarin uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa zargin sa da zambar makudan kudi mallaki wasu fitattun Mutane na kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel