Dukkan 'yan takarar PDP sun fi Buhari cancanta - Dankwambo

Dukkan 'yan takarar PDP sun fi Buhari cancanta - Dankwambo

- Gwamna Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe ya ce dukkan 'yan takarar shugabancin kasa na PDP sun fi shugaba Buhari cancanta

- Dankwambo ya ce sun fi shugaba Buhari cancanta ne saboda sun samu tarbiyya daga jam'iyyar PDP

A yau, Litinin ne gwamna jihar Gombe kuma daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Ibrahim Dankwambo ya ce dukkan masu neman takarar shugabancin kasa a PDP sun fi shugaba Muhammadu Buhari cancanta.

Gwamnan ya yi wannna jawabin ne a jihar Plateau a sakatariyar PDP yayin da ya ke yakin neman zabensa gabanin zaben fidda gwamni da jam'iyyar za tayi a cikin watan Satumba.

Dukkan 'yan takarar PDP sun fi Buhari cancanta - Dankwambo
Dukkan 'yan takarar PDP sun fi Buhari cancanta - Dankwambo
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Atiku ya bayyana sababbin rikicin makiyaya da manoma a Benue

A halin yanzu jam'iyyar PDP tana da masu neman takara 13 cikinsu har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsaffin gwamnoni; Rabiu Musa Kwankwaso, Sule Lamido, Jonah Jang, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, gwamnan jhar Sokoto, Aminu Tambuwal da sauransu su.

Dankwambo ya shawarci dukkan sauran 'yan takarar su marawa dukkan wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwanin baya domin a cewarsa dukkansu su fi shugaba Muhammadu Buhari cacantan jagorancin ragamar mulkin kasar.

"Mun kai misalin 13 da ke neman takarar shugabancin kasa a PDP kuma kowanne cikinmu ya fi Buhari cancanta domin jam'iyyar mu mai daraja tayi mana tarbiya ta yadda za mu iya ceto Najeriya daga halin da ta shiga. Mun samu tarbiyya daga jam'iyyar mu," inji Dankwambo.

Dankwambo kuma ya shaidawa 'yan jam'iyyar cewa idan aka zabe shi zai samar da ilimi kyauta kana zai inganta batun tsaro a dukkan jihohin Najeriya kamar yadda ya yi a jiharsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel