Mace mau dauke da juna biyu, mijinta, da dansu sun mutu sakamakon abinci mai guba

Mace mau dauke da juna biyu, mijinta, da dansu sun mutu sakamakon abinci mai guba

Wata mata mai dauke da juna biyu tare da Maigidanta da kuma wani karamin yaro mai shekaru goma duk sun rasa rayuwarsu a sanadiyyar cin abinci mai guba a unguwar Swali dake garin Yenegoa na jahar Bayelsa, inji rahoton jaridar Sahara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito makotane suka gano gawar matan mai suna Nkem Igwenta, Mijinta Orji Igwenta da kuma dan kaninta mai shekara goma Obinna Ogbani, har ma da wani bera da yacin abincin a cikin dakinsu.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya kammala shirin daukan sabbin malaman asibiti 3,059 a Kaduna

Sai dai abin mamakin shine matar mai dauke da juna biyu ce ta shirya abincin, don haka aka rasa ta yaya gubar ta shiga cikin abincin nasu, sai dai kwatsam aka tsinci gawarwakinnasu kwance a cikin dakinsu.

Wani dan kasuwa dake unguwar, ya tabbatar da mutuwar iyalan, inda yace: “Mummunan bala’I ya afka mana a titin winners, unguwar Swali, mun kadu sosai da mutuwar iyalan gaba daya.

“Abin dake kara bamu mamaki shine ta yadda gubar ya shiga cikin abincinnasu, amma Allah zai saka musu idan har wani mutum ne yayi musu wannan muguntar.” Inji shi.

Itama rundunar Yansandan jahar ta bakin kaakakinta, Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace “Maigidan da mamatan ke haya ne ya kai fara kai kara ga yansanda cewa Orji da matarsa Nkem da wani karamin yaro dan uwansu dake zama dasu sun mutu a cikin dakinsu.

“Haka zalika an gano gawar wani bera a dakinnasu da ake zaton shima gubarce ta yi ajalinsa bayan ya tsoma bakinsa a cikin abincin.” Inji Kaakaki Butswat.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel