Osun 2019: Buhari ya cancanci a yaba mai a duk yadda sakamakon zaben zai zo

Osun 2019: Buhari ya cancanci a yaba mai a duk yadda sakamakon zaben zai zo

Bayan cewa da hukumar zabe mai zaman kanta tayi ba’a kammala zaben gwamnan jihar Osun ba, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci a yaba masa, jaridar Vanguard ta ruwaito.

A wani jawabi ga manema labarai, shugaban hukumar na jihar, Joseph Adeola Fuwape, ya bayyana cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana rashin kammala zabe saboda tazara da dan takaran jam’iyyar PDP, Ademola Adeleke ya baiwa dan takaran APC.

A hilin yanzu, hukumar INEC ta sanya ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba, a matsayin ranar sake zaben gwamna, shawarar wanda yawancin yan Najeriya, musamman akan shafukan zumunta suka nuna rashin amincewa.

Duk da haka, wasu masu lura sun yabi hukumar INEC akan nasarar da ta cimma wajen gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsohon hadimin Oshiomhole ya sauya sheka zuwa PDP da dubban magoya bata

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party na iya kulla yarjejeniya da tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore a kokarinsu na son lashe zaben gwamna a jihar wanda za’a sake gudanarwa a ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.

Omisore ya kasance dan takarar gwamna a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben wanda dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke ya zo na farko da kuri’u 254, 698, yayinda dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mista Gboyega Oyetola, ya zo na biyu da kuri’u 254,345.

Hukumar zabe mai zaman kanta tace za’a sake zabe a wasu mazabu inda aka soke zabuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel