Uwar jam’iyyar APC ta dage ranar gudanar da zaben fidda gwani na mukamin shugaban kasa

Uwar jam’iyyar APC ta dage ranar gudanar da zaben fidda gwani na mukamin shugaban kasa

Uwar jam’iyyar APC ta kasa, ta sanar da dage ranar data sanya a baya da zata gudanar da zaben fidda gwani na masu muradin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin inuwarta, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jam’iyyar ta canza ranar yin zaben daga ranar 25 ga watan Satumba zuwa ranar 27 ga watan Satumba, kimanin karin kwanaki biyu kenan, kamar yadda kaakakin jam’iyyar Yekini Nabena ya bayyana.

KU KARANTA: Takarar shugaban kasa: APC ta jahar Filato ta bayyana goyon bayanta ga Buhari

Kaakaki Yekini ya fitar da wannan sanarwar ne a ranar Lahadi, 23 ga watan Satumba, inda yace uwar jam’iyyar ta yanke wannan shawarar ne don baiwa sauran yayan jam’iyyar APC damar karbar katinsu na zaba yayan jam’iyya a mazabunsu.

Ita dai jam’iyyar APC ta bayyana tsarin fitar da gwaninta a matakin kujerar shugaban kasa a matsayin kato bayan kato, inda yayan jam’iyya zasu saka layi su kada kuri’a don fitar da dan takarar da zai wakilceta a babban zaben shugaban kasa na 2019.

Sai dai a wani hannun kuma uwar jam’iyyar ta baiwa gwamnonin APC su ashirin da uku damar su zabi tsarin zaben fidda gwanin da suke ganin ya dace dasu a wajen fitar da yan takarkarun duka mukamai banda na shugaban kasa.

Amma wannan matakin da APC ta dauka ya janyo cece kuce daga sauran yan siyasa musamman Sanatoci dake hamayya da gwamnonin jihohinsu, inda suke ganin kamar jam’iyyar ta baiwa gwamnonin lasisin yin kama karya kenan a jihohinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel