Takarar shugaban kasa: APC ta jahar Filato ta bayyana goyon bayanta ga Buhari

Takarar shugaban kasa: APC ta jahar Filato ta bayyana goyon bayanta ga Buhari

Uwar jam’iyyar APC ta jahar Filato ta bayyana goyon bayanta ga takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin a kokarinsa na zarcewa a kujerar shugaban kasar Najeriya karo na biyu.

Legit.ng ta ruwaiti uwar jam’iyyar ta jahar Filato ta tabbatar da wannan goyon baya ne a yayin wani zama na musamman data gudanar da shuwagabannin jam’iyyar, ciki har da gwamnan jahar Simon Bako Lalong da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

KU KARANTA: Ashura: Yan shia sun yi arangama da jami’an tsaro a Potiskum 1 ya mutu 3 sun jikkata

Takarar shugaban kasa: APC ta jahar Filato ta bayyana goyon bayanta ga Buhari
Taron
Asali: Facebook

Kaakakin gwamnatin jahar Filato, Yakubu Dati ne ya sanar da wannan matakin da jam’iyyar APC ta dauka, inda yace wannan taro na musamman ya gudana ne a garin Pankshin dake yankin Filato ta tsakiya.

Idan za’a tuna dai a kwanakin baya ne wasu matasa masu kishin kasa suka yankan ma shugaba Buhari tikitin sake tsayawa takarar shugaban kasa akan kudi naira miliyan Arba’in da biyar (N45, 000, 000) kuma suka mika masa jin kadan bayan ya dawo daga kasar China.

Legit.ng ta tabbatar da tun bayan da matasan suka sayan ma Buhari tikitin babu wani mai burin taka takarar shugaban kasa a cikin jam’iyyar APC daya sake sayan wannan takardar takara, wanda hakan ke nuna kamar dama shi kadai jam’iyyar ta yi nufin sayar ma tikitin.

A wani labarin kuma rahotanni sun nuna uwar jam’iyyar APC ta kasa a karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar, tsohon gwamnan jahar Edo Adams Oshiomole ta sanar da dage zaben fidda gwani na mukamin shugaban kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng