Zaben Osun: Ma’aikacin INEC ya gudu da sakamakon mazaba guda, sakamakon Osogb

Zaben Osun: Ma’aikacin INEC ya gudu da sakamakon mazaba guda, sakamakon Osogb

Jami’in tattara sakamakon zabe ya bayyana cewar daya daga cikin ma’aikatan da suka gudanar da zaben gwamnan jihar Osun a jiya, Asabar, ya tsere da sakamako da kayan aikin zaben wata mazaba guda.

A yayin da ake dakon sakamako daga babban birnin jihar Osun, Osogbo, mai yawan jama'a, yanzun haka sakamakon ya shigo hannu.

OSOGBO

APC - 23,379

ADP - 2478

PDP - 14,499

SDP - 10,188

ADC - 413

Sai dai sakamakon na Osogbo ya canja yadda nasarar jam'iyyu ke tafiya a sakamakon zaben da aka saki zuwa yanzu.

A baya Legit.ng ta sanar da ku cewar sakamakon Karamar Hukuma guda kadai ya rage a gane wanda zai lashe zaben Jihar Osun. Wannan Karamar Hukuma dai ita ce Osogbo inda nan ne babban Birnin Jihar Osun kuma mafi yawan Jama’a a kaf Jihar.

Zaben Osun: Ma’aikacin INEC ya gudu da sakamakon mazaba guda, sakamakon Osogb
Cibiyar tattara sakamakon gwamnan jihar Osun
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa da zarar an samu cikakken sakamakon Garin Osogbo za a gane wanda zai zama sabon Gwamnan Jihar Osun. Yanzu dai an kawo sakamakon kananan Hukumomi 29 cikin 30 da ake da su.

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa APC tana da kuri’u 224, 488 yayin da Jam’iyyar adawa na PDP ke da kuri’a 236, 784. Hakan na nufin PDP ta sha gaban APC da kuri’a 12, 000. Yanzu dai sakamakon Osogbo kurum ake sa rai ya fito.

DUBA WANNAN: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam'iyyunsu, hotuna

Jam’iyyar APC ta samu nasara a Kananan Hukumomi 15 yayin da PDP ta lashe Kananan Hukumomi 11 kacal. ADP kuma ta samu nasara a Karamar Hukumar Iwo yayin da SDP ta kawo Kananun Hukumomin Ife ta tsakiya da Gabas.

A Garin na Osogbo dai ana iya samun kuri’u fiye da 50, 000 wanda hakan ya sa PDP ta fara kukan murdiya tuni. Idan har APC ta kerewa Jam’iyyar PDP da kuri’a fiye da 12, 000 a nan, to za ta lashe zaben inda za ta cigaba da mulkin Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng