Wata sabuwa: An koma sayar kuri'a ta hanyar aika kudi ta wayar hannu - INEC

Wata sabuwa: An koma sayar kuri'a ta hanyar aika kudi ta wayar hannu - INEC

- Lamarin cinikin kuri'a ya dau sabon salo mai tayar da hankali

- Yanzu 'yan siyasa sun koma amfani da wayoyin salula wajen cinikayyan kuri'ar

- Ciyaman din INEC, Mahmmod Yakubu ne ya bayyana wannan sabon hanyar sayar kuri'ar

Ciyaman din hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ta gano cewar yanzu masu sayar kuri'a sun dena zuwa da tsabar kudi wajen zabe sai dai sun koma amfani da wayar salula wajen sayan kuri'un a ranar zabe.

Wata sabuwa: An koma sayar kuri'a ta hanyar aika kudi ta wayar hannu - INEC
Wata sabuwa: An koma sayar kuri'a ta hanyar aika kudi ta wayar hannu - INEC
Asali: Depositphotos

Farfesa Yakubu ya yi wannan jawabin ne a ranar 20 ga watan Satumba yayin da ya ke ganawa da kwamishinonin EFCC na kasa domin gano hanyoyin da za'a bi domin magance wannan sabuwar matsala da ta bullo.

DUBA WANNAN: Jihohin da APC bata da hamayya mai karfi, kamar yadda yake a Aso Rock - Ahmad

"Abinda ke gaban mu shine zaben Osun wanda daga shi sai babban zaben 2019. Mun fara daukan matakai a matsayin mu na hukuma amma muna bukatar taimakon hukumar EFCC domin magance wannan matsalar." inji Mahmood.

A wata rahoton, Legit.ng ta samu daga The Nation cewa 'yan sanda sun kama mutane biyu da ke sayar kuri'a a zaben gwamna da ake gudanarwa yau Asabar 22 ga watan Satumba a jihar Osun.

Hukumomin tsaro ciki har da EFCC sun gargadi mutane kan mummunar dabi'ar ta cinikin kuri'u a inda suka dau alwashin hadin gwiwa da INEC domin kawo karshen lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel