Abin kunya: Kotu ta kashe auren ma’aurata bayan Miji ya dirka da ma yan aikinsu ciki sau 2

Abin kunya: Kotu ta kashe auren ma’aurata bayan Miji ya dirka da ma yan aikinsu ciki sau 2

Wata karamar kotu dake garin Gudu na babban birnin tarayya Abuja ta sanar da kashe auren wasu ma’aurata da suka kwashe tsawon shekaru biyun suna zaman lafiya sakamakon Mijin ya tafka abin kunya, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito uwargida mai suna Doyinsola Adebiyi ce ta shigar da karar mijinta Adebiyi Kayode sakamakon yana neman yar aikinsu da zina a gidansu dake rukunin gidajen gwamnatin tarayya dake Lugbe cikn garin Abuja.

KU KARANTA: Jerin wasu manyan ministoci guda 3 da suka ajiye aikinsu a gwamnatin Buhari

Uwargida Doyin ta shaida ma Kotun cewa yar aikinnata da kanta ta tabbatar mata da cewa mijin na nemanta kuma ma har ya dirka mata ciki sau biyu, amma ta zubar dasu duka, haka zalika a yanzu haka yar aikin na dauke da cikin Mijinnata dan wata uku.

Doyin ta bayyana ma kotu cewa: “Bayan da na samu labarin abin mijina yake aikatawa ne sai ba fice daga gidanmu dake Lagos na dowa Abuja, amma kimanin watanni biyu kenan mijin nawa bai neme ni ba, har ma na samu labarin ya kara aure, ya auri budurwa yar shekara 20.”

Sai dai shima gogannaku, Kayode Adebiyi mai shekaru 51 ya aika ma Kotun wasika ta hannun lauyansa, inda ya roki kotu data biya ma matarsa bukatar da take nema a wajenta, ma’ana shima ya goyi bayan a kashe auren nasu.

Kayode ya bayyana ma Kotu cewa tunda dai Doyin ta iya barin gidan aurenta ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, toh shima baya bukatar cigaba da zama da ita, don haka Kotu ta kashe auren kawai.

Daga karshe Alkali Abdul Bello ya biya ma ma’auratan bukatarsu, ya kashe auren domin kowa ma ya huta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel