Bafarawa ya bayyana dalilin da ya sanya yake son kasancewa shugaban kasar Najeriya

Bafarawa ya bayyana dalilin da ya sanya yake son kasancewa shugaban kasar Najeriya

A ranar Larabar da ta gabata ne daya daga cikin manema takarar kujerar shugaban kasa a karshin jam'iyyar adawa ta PDP, Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewa ya na hankoron kujerar ne ba da wata manufa ta karan kansa ba sai don kishin yiwa kasar nan hidima.

Tsohon gwamnan na jihar Sakkwato, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da mambobin jam'iyyar ta PDP a jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Bafarawa ya ziyarci jihar ta Legas ne yayin ci gaba da yawon shawagi da karade kasar nan dangane da neman goyon baya kan kudirinsa na hankoron kujerar shugaban kasa.

Bafarawa ya bayyana dalilin da ya sanya yake son kasancewa shugaban kasar Najeriya
Bafarawa ya bayyana dalilin da ya sanya yake son kasancewa shugaban kasar Najeriya
Asali: Depositphotos

Yake cewa, kasar nan ta na da bukatar shugaba mai cikakkiyar wayewa ta fuskar jagoranci gami da tabbatuwar zakakuranci da kwarewa domin tunkarar kalubalan da kasar nan take fuskanta a halin yanzu.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa, jam'iyya mai ci ta APC ta gaza ta kowace fuska wajen cika alkawurranta na canji wajen ceto kasar nan daga halin da ta ke ciki.

KARANTA KUMA: Rai daya ya salwanta yayin da 'Yan Baranda suka kai hari Birnin Gwari

Bafarawa ya ci gaba da cewa, zamaninsa akan kujerar gwamnatin jihar Sakkwato ta yi zarra da fintinkau a tarihin jihar ta fuskar tabbatar da kwarara da kuma sharbar romo na dimokuradiyya.

Ya kara da cewa, bai inganta jihar Sakkwato ta fuskar tattalin arziki kadai ba, sai dai ya kuma inganta jin dadin al'ummar jihar ta fuskar harkokin lafiya da kuma ilimi.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tarihi ba zai mance da yadda Bafarawa ya gudanar da shugabanci a jiharsa ba tare da cin bashi ko na sisin Kobo sai ma N13bn da ya bari cikin asusun gwamnatin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel