'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya

'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya

- Mai bawa gwamnan jihar Delta shawara kan saka hannun jari ya rasu

- Wasu 'yan bindiga ne suka kashe Mr Sunday Ozege a titin Benin zuwa Edo

- Gwamnan jihar ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin da mutanen jihar baki daya

A ranar Talata ne wasu 'yan bindiga da ba'a gano ko su wanene ba suka harbe mai bawa gwamnan jihar Delta shawara kan harkokin saka hannun jari, Mr Sunday Ozege a babban titin Benin.

A sakon ta'aziyya mai dauke da sa hannun sakataren yadda labarai na jihar, Charles Aniagwu, gwamnan ya yiwa iyalan marigayi Ozege da ke karamar hukumar Ndokwa ta Yamma ta'aziyya inda ya yi fatan Allah ya gafarta masa.

'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya
'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

Gwamnan ya ce marigayin mutum ne mai kwazo wajen aiki kuma yana da hulda mai kyau da jama'a.

Kazalika, gwamnan ya bayyana Mr Ozege a matsayin abin dogaro musamman a cikin ayyuka da dama da ya yi a kwamitocci da yawa a lokacin da ya ke raye.

"Nayi jimamin samun labarin rasuwar Mr Sunday Ozege a hannun wasu 'yan bindiga a babban titin Benin zuwa Edo. Mutane da dama za suyi rashinsa saboda irin kyawawan halayensa.

"Muhimmiyar rawar da ya taka a siyasa da cigaban yankinsa a jihar zai sama abin koyi ga sauran 'yan siyasa masu tasowa.

"Ina mika son ta'aziyya ta ga iyalansa da mambobin kwamitin zartarwa na jiha da kuma mutanen Ogume," inji Gwamnan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel