Har yanzu dan na da ya mutu na amfani da bandakinmu kowanne dare - Mahaifiya

Har yanzu dan na da ya mutu na amfani da bandakinmu kowanne dare - Mahaifiya

- Wata mata tayi ikirarin cewa fatalwar dan ta na zuwa gidan ta duk dare domin amfani da ban daki

- Matar ta ce fatalwan yana damun ne ta ne saboda ba'a kawo mata dan ta ta ga gawarsa kafin a birne shi ba

- Sai dai wani Fasto a garin ya ce aljannu ke damun matar ba fatalwan dan ta ba

Wata mace 'yar Afrika ta Kudu mai suna Ntombosindiso Thuthani ta koka kan yadda fatalwan dan ta ke zuwa gidan cikin dare yana damun ta. Cikin damuwa Thutani da ta ce fatalwan na zuwa amfani da ban daki da ke gidan duk dare.

Fatalwar dana tana zuwa bandaki bayan munyi bacci - Wata mai makokin danta
Fatalwar dana tana zuwa bandaki bayan munyi bacci - Wata mai makokin danta
Asali: UGC

Ta ce fatalwan yana zuwa gidan ta ne saboda ba'a yi masa jana'iza irin wadda ta dace ba. Ta kara da cewa ba'a kawo mata gawan danta zuwa kauyensu a Marikana da ke Capetown ba kafin a birne shi.

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

An ruwaito cewa an tafi da gawar yaron mai shekaru 17 ne zuwa garin Eastern Cape inda aka birne shi hakan ya sa duk dare fatalwansa ke zuwa gidanta yana damunta.

Thuthani ta ce ranar da abin ta fara, ta ji an kwankwasa kofar gidanta cikin dare amma idan ta tambaya wane ke kwankwasa kofar sai a amsa da cewa ta bude kofa. Daga nan kuma sai ta ji motsin mutum yana tafiya ban dakinta.

Wadannan abubuwan mamakin da ke faruwa ya sanya ta ziyarci wani boka wanda ya ce mata sai anyi wasu ayyuka kafin fatalwan Yamkela zai dena zuwa gidan ta. Bokan ya ce ko da ta canja gida fatalwan za ta cigaba da bin ta muddin ba ayi abinda ya kamata ba.

Sai dai wani fasto ya ce ba fatalwar dan ta bane ke damunta, ya ce shedanun aljannu ne kuma ya kamata tayi addu'o'i saboda ta kare kanta daga masifar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel