Abubuwa 5 da Buhari ya fada a wurin yakin neman zaben APC a jihar Osun

Abubuwa 5 da Buhari ya fada a wurin yakin neman zaben APC a jihar Osun

A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnonin APC 13 da kuma jiga-jigan jam’iyyar suka dira jihar Osun domin yakin neman zaben dan takarar gwamnan Osun a karkashin tutar jam’iyyar APC, Alhaji Gboyega Oyetola, a zaben da za a yi ranar Asabar, 22 ga wata Satumba.

Yayin jawabinsa, shugaba Buhari ya yi wasu muhimman kalamai ga jama’ar da suka halarci taron da kuma ragowar masu kada kuri’a a zaben shekarar 2019. Ga wasu daga cikin muhimman abbuwa da Buhari ya fada a jawabinsa:

Abubuwa 5 da Buhari ya fada a wurin yakin neman zaben APC a jihar Osun
Abubuwa 5 da Buhari ya fada a wurin yakin neman zaben APC a jihar Osun
Asali: Twitter

1) Shugaba Buhari ya bayyana jihar Osun a matsayin jihar APC tare da bukatar mutanen jihar su cigaba da goyon bayan APC

2) Shugabanh kasar ya yiwa mutanen jihar Osun kaimi a kan zaben APC a zaben ranar Asabar tare da jan hankalinsu a kan biyewa mayaudara dake son mayar da jihar ta Osun koma baya

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

3) Buhari ya nanata kudirin gwamnatinsa na kamala dukkan manyan aiyukan da gwamnatin tarayya ke shimfidawa a jihar da suka hada da ginin hanyar Gbongan zuwa Ibadan, hanyar Ejigbo zuwa da ta Ondo zuwa Ife.

4) Shugaba Buhari ya shaidawa jama’ar jihar cewar gwamnatinsa zata cigaba da yaki da cin hanci da rashawa

5) Buhari ya tunawa masu kada kuri’a cewar burin APC shine gina Najeriya da kowa zai mori gwamnati ba wai iya wasu tsirarun shafaffu da mai ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel