Taron dangi: Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira, hotuna

Taron dangi: Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira, hotuna

A yau, Talata, hukumar soji ta fitar da sanarwar cewar dakarun sojin Najeriya na runduna ta 21 dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno tare da hadin gwuiwar dakarun sojin kasar Cameroon suka kasha mayakan kungiyar Boko Haram 5 a kauyukan Yabiri kote da Bula Dadobe dake kan iyakar Najeriya da Cameroon ta karamar hukumar Bama.

Sojojin sun yi aikin hadin gwuiwa ne karkashin ofireshon “RAINBOW 15” bayan gano cewar mayakan kungiyar Boko Haram sun mayar da sansaninsu kan tsaunikan dake kauyukan Yabiri Kote da Bula Dadode, inda suke shirya hare-haren da suke kaiwa kauyukan dake Najeriya da Cameroon.

Yayin atisayen sojin na hadin gwuiwa, dakarun soji sun kwashe wasu makaman mayakan kungiyar ta Boko Haram da suka hada da: bindiga kirar AK47 guda 3, Babur 2, Bam 2 da jigidar harin kunar bakin wake.

Taron dangi: Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira, hotuna
Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira
Asali: Twitter

Taron dangi: Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira, hotuna
Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira
Asali: Twitter

Ko a ranar Lahadi saida dakarun rundunar soji ta 22 dake aikin kakkabe ragowar mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno suka yi wani kazamin artabu da mayakan kungiyar Boko Haram.

DUBA WANNAN: A kori ta'addanci: Hukumar sojin sama ta samu karin sabbin jiragen yaki 30

Mayakan kungiyar ta Boko Haram ne suka fara kai wa dakarun sojin harin kwanton bauna yayin da suke kan hanyar su ta zuwa Bama daga Maiduguri. Sai dai reshe ya juye da mujiya domin sojojin sun yi nasara a kan 'yan ta'addar bayan musayar wuta ta dan takaitaccen lokaci.

Dakarun sojin sun kashe dukkan mayakan kungiyar ta Boko Haram da suka kawo masu harin tare da kwashe dukkan makamansu.

Taron dangi: Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira, hotuna
Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira
Asali: Twitter

Taron dangi: Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira, hotuna
Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira
Asali: Twitter

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel