Ziyarar Theresa May: Gwamnatin Ingila tayi furuci a kan takarar Buhari da APC ba zata so ba
- A kwanakin baya-bayan nan ne Firaminstar kasar Ingila, Theresa May, ta kawo wata ziyarar aiki Najeriya
- Ziyarar ta Theresa May ta jawo barkewar cece-kuce a tsakanin manyan jam’iyyun Najeriya, musamman tsakanin APC mai mulki da PDP, mai adawa
- A yau, Litinin, gwamnatin kasar Ingila, ta hannun ofishin jakadancinta dake Najeriya, tayi Karin haske, domin cireshakku a kan batun ziyarar ta Firaminsta May
Babban ofishin jakadancin kasar Ingila dake Najeriya y ace ziyarar da firaminastar kasar, Theresa May, ta kawo kwanakin baya bat a da alaka da nuna goyon baya ga takarar shugaba Buhari ko wani dan takara.
Laura Beaufils, mataimakiyar jakadan kasar Ingila a Najeriya, ce ta bayyana hakan yau a Legas yayin amsa tambayoyi daga manema labarai.
Laura ta jaddada niyyar kasar Ingila ta kasha Yuro miliyan #47.4 domin karfafa dimokradiyya a Najeriya karkashin manufar kasar na karawa siyasa karfi a Najeriya zagaye na 2 (DDiN2).
DUBA WANNAN: Sule Lamido ya lissafa mutane 4 da suka fi Buhari kima da gaskiya
Da ta ke bayani a kan rawar da kasar Ingila ke takawa domin karfafa harkokin siyasa a Najeriya, Laura, ta ce gwamnatin Birtaniya ba tad a niyyar canja zabin mutanen Najeriya a zabukan shekarar 2019.
Wannan mataki ya yiwa wani bangare na masu son yin takarar shugaban dadi, musamman bangaren ‘yan takarar jam’iyyar PDP dake ganin cewar gwamnatin Ingila ta karkata a kan takarar shugaba Buhari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng