2019: Hikimar Ganduje na zaben Nasiru Gawuna a matsayin sabon mataimakinsa

2019: Hikimar Ganduje na zaben Nasiru Gawuna a matsayin sabon mataimakinsa

- Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya zabi kwamishinansa na noma ya zama sabon mataimakinsa

- Mai taimakawa gwamna Ganduje a bangaren yada labarai, Salihu Tanko Yakasai, y ace tuni gwamnan na Kano ya mika sunan Gawuna ga majalisar dokokin jihar

- Idan majlisar dokokin jihar Kano ta amince, Gawuna zai maye gurbin tsohon mataimakin gwamna Ganduje da ya yi murabus, Farfesa Hafiz Abubakar

A jiya, Lahadi, ne kafafen yada labarai suka wallafa rahoton cewar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya zabi kwamishinansa na noma, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin sabon mataimakinsa.

A yau, Litinin, ne Salihu Tanko Yakasai, mai taimakawa gwamna Ganduje a bangaren yada labarai, ya bayyana cewar tuni gwamnan ya mika sunan Gawuna ga majalisar dokokin jihar Kano domin neman sahalewar su.

Zabin Gawuna a matsayin sabon mataimakin gwamnan na Kano, ya bawa wasu jama’a da dama mamaki saboda an yi tsammanin Ganduje zai fitar da mataimaki ne daga cikin manyan ‘yan siyasar da suka canja sheka tare da Shekarau daga PDP zuwa APC.

2019: Hikimar Ganduje na zaben Nasiru Gawuna a matsayin sabon mataimakinsa
Ganduje da Nasiru Gawuna
Asali: Facebook

Wasu ma ganin cewar da Malam Salihu Sagir Takai, na hannun dammar Shekarau ya dawo APC da shine Ganduje zai dauka a matsayin mataimaki. Sai dai masu nazarin siyasar Kano sun ce koda Takai din ya dawo APC, ba zai samu kujerar mataimaki ba tare da bayyana cewar sanin hakan ne ma ya sa Takai ya ki biyo Shekarau zuwa APC.

Masu nazarin siyasar sun bayyan cewar ya zama dole Ganduje ya dauko mataimaki daga Kano ta tsakiya matukar yana bukatar samun nasara cikin sauki a zaben shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Annoba: Mummunar ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 31, ta rsuhe gidaje fiye da 10,000 a Kano

Kazalika, sun bayyana cewar Ganduje ya yi lissafi mai kyau ta hanyar dauko daya daga cikin yaransa daga cikin birnin Kano domin ya zama mataimakinsa domin hakan zai jawo masa saukin yakin zabe a cikin kwaryar garin Kano mai tarin miliyoyin masu kada kuri’a.

Idan majlisar dokokin jihar Kano ta amince, Gawuna zai maye gurbin tsohon mataimakin gwamna Ganduje da ya yi murabus, Farfesa Hafiz Abubakar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel