Mutane 3,487 sun samu dubu biyar biyar na Baba Buhari a karamar hukuma daya ta Jahar Jigawa

Mutane 3,487 sun samu dubu biyar biyar na Baba Buhari a karamar hukuma daya ta Jahar Jigawa

Akalla mutane dubu uku da dari hudu da tamanin da bakwai ne suka ci moriyar tsarin rabon naira dubu biyar biyar wanda gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a karamar hukumar Kaugama ta jahar Jigawa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dubunnan mutanen sun samu wannan tagomashi ne a karkashin tsarin jiyar da yan Najeriya dadi da Buhari ya kirkiro da ake yi ma taken ‘Conditional cash transfer-CCT’ a turance.

KU KARANTA: Shamsuna Ahmad ta kama aiki gdan gadan a matsayin sabuwar ministar kudi

Mataimakin shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Abdulhamid ne ya bayyana haka a yayin dayake jawabi a taron wayar da kawunan mutanen da suka amfana da tsarin game da muhimmancin wannan kudi a ranar Litinin a garin Taura.

Mutane 3,487 sun samu dubu biyar biyar na Baba Buhari a karamar hukuma daya ta Jahar Jigawa
Naira
Asali: Depositphotos

Ahmed yace an zabo mutanen ne daga mazabun Jibrin, Jae, Dabuwaran, Girbobo, da Yalo, sa’annan ya jinjina ma gwamnatin tarayya game da kirkiro wannan tsarin na tallafa ma gajiyayyu da marasa karfi, kuma yayi alkawarin bada goyon bayan ganin an tabbatar da tsarin.

A nasa jawabin, shugaban aikin rabon kudin CCT na jahar Jigawa, Ibrahim Rabakaya ya bayyana cewa an samar da tsarin ne domin tallafa ma talakawa, da gajiyayyu dake cikin al’umma, domin su samu tsayawa da kafafuwansu.

Sai dai Rabakaya ya bayyana sharuddan da gwamnati ta gindaya kafin mutum ya fara amsan wannan kudi na naira biyar da suka hada da shaidar yin allurar rigakafi, halartar kulawar bayan haihuwa a asibiti da kuma tsaftace muhalli.

Daga karshe shima hakimin Tauran Yamma, Alhaji Tijjani Haruna yayi kira ga karamar hukumar Kaugama data dada wayar da kawunan al’umma game da tsarin don kare jama’a daga ayyukan macuta da yan damfara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel