Da duminsa: Ministar kudi, Kemi Adeosun, ta sulale bayan yin murabus

Da duminsa: Ministar kudi, Kemi Adeosun, ta sulale bayan yin murabus

Tsohuwar minstar kudi, Kemi Adeosun, ta fice daga Najeriya kwana daya kacal bayan ta mika takardar barin mukaminta biyo bayan samunta da laifin karyar takardar bautar kasa.

Adeosun ta kasance ministar kudin Najeriya tun watan Nuwamba na shekarar 2015. Ta yi murabus daga mukaminta ne bayan jaridar Premium Times ta bankado cewar ministar ta gabatar da takardar bauatr kasa ta bogi.

A jiya Jum'a, 14 ga watan Satumba, Mrs. Kemi Adeosun ta yi murabus daga kujerarta ta Ministar kudi, biyo bayan zarginta da ake yi na amfani da takardar shaidar yin bautar kasa ta bogi.

Wannan zargi ya dauki tsawon lokaci yana yawo a tsakanin jama'a, har sai ranar juma'a da Kemi ta kawo karshen shi ta hanyar sauka daga mukamin.

Karanta cikakkiyar wasikar da ta aikawa shugaban kasa Buhari, don sanar da shi matsayarta na yin murabus daga wannan mukami na ministar kudi.

Da duminsa: Ministar kudi, Kemi Adeosun, ta sulale bayan yin murabus
Kemi Adeosun
Asali: UGC

Wasikar na cewa:

Zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Bari na fara da yin godiya a gareka bisa bani dama don yin shugabanci a karkashin mulkinka.

Hakika na samu tarin ilimi da basirori sosai daga gareka, tare da gano hakikanin karkonka. A yau, na samu kaina a cikin komar bincike da zargi akan cewa ina amfani da takardar bautar kasa ta jabu. Ko a wancan lokacin, na shiga damuwa matuka, duba da manufofin wannan gwamnati na samar da nagarta, ya zamar min wajibi in dau hukuncin da ya dace, wato in yi murabus.

Ranka ya dade, ina so ka bani dama don zayyana maka kadan daga yadda lamari ya samo asali. Ni dai an haife ni a Burtaniya kuma a can na girma, hakika gidan iyayena har gobe na can Landan ne. Idan kaga na zo Nigeria a cikin shekaru 34, to nazo hutu ne kawai, ko a lokacin takardar Fasfo dina ta kasar Burtaniya ce. Na samu fasfo na Nigeria a lokacin ina da shekaru 34 kuma a lokacin da na dawo kasar an samu takaddama kan batun bautar kasa.

DUBA WANNAN: An sayi hoton El-rufa'i da dalibi ya zana cikin minti 2 a kan miliyan N2m

Da na bincika sai na gano cewa ba zan iya yin bautar kasa ba kasancewar shekaruna sun haura 30 kuma ba a kasar na ke da zama ba. Ni dai na tafi akan hakan, har sai da wancan zargi ya taso. Bisa tafiya akan shawarwari da taimako daga wadanda na ke tunanin masu amana ne, an tuntubi hukumar NYSC don bani takardar yin bautar kasa. Jim kadan aka bani wannan takarda. La'akari da cewa ban taba yin aiki a NYSC ba, ban ma taba zuwa harabar hukumar ba, ban san yadda suke gudanar da aikinsu ba, hakika ba zan samu wata masaniya akan takardar ta gaskiya ce ko ta bogi ba.

Shekara ta 2011 na gabatar da takardar a gaban majalisar dokoki ta jihar Ogun domin tantance ni, haka ma a shekara ta 2015 na gabatar da ita a gaban hukumar DSS don tantance ni, har na gabatar da ita a gaban majalisar wakilai ta tarayya. Ba tare da sauran ja-in-ja ba, a matsayina na wacce ta ke riko da al'adar yin gaskiya da bin kadinta, na yanke shawarar sauka daga wannan mukami nawa, daga yau Juma'a, 14 ga watan Satumba, 2018.

Ranka ya dade, hakika abun alfahari ne a gare ni, na yin aiki ga kasata kuma a karkashin mulkinka, wanda ya bani damar taka rawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar cikin karamin lokaci duk da kalubalan da aka fuskanta. Ina alfahari da cewar Nigeria ta kawo gyara a sha'anin kudinta, kuma ta gano tare da bin hanyoyi na dorewar bunkasar tattalin arzikinta.

A karkashin mulkinka, Nigeria ta fice daga jerin kasashen da ke fama da talauci har ma ta fara aza harsashen dorewar bunkasar tattalin arzikinta. Hakika sake fasalin tattalin arziki ba wai abu ne mai sauki ko wanda za a yi a kankanin lokaci ba.

Haka zalika, akwai wasu matakai da ya kamata a dauka amma na san cewa tunaninka na saka hannun jari, tattara haraji da kuma smarwa kudi daraja a harkokin kasuwanci zai habbaka arziki da kuma samun dama ga yan Nigeria.

Ina godiya ga shugaban kasa, mataimakinsa da kuma abokanan aiki na majalisar zartaswa ta kasa bisa damar da na samu na yin aiki tare da su. Ina kuma godiya musamman ga ma'aikatan ma'aikatar kudi, kama daga mashawarta da kuma shuwagabanni sashe sahe na ma'aikatar.

Ranka ya dade, wadannan mutane sun fito daga kabilu daban daba, nasabar su ba daya ba ce, haka zalika shekarunsu ba daya bane. Sun yi aiki tukuru, don agaza mani wajen aiwatar da ayyukan da suka rataya a kaina. Kwazon ma'aikata na da kuma damarsu ta yin aiki a tare don cimma manufa daya ya tabbatar mun da cewa Nigeria na da dukkanin karfin dan Adam na samun nasara a kowane fanji.

Ranka ya dade, bari na karkare ta hanyar jinjinawa hakuri da goyon bayanka, a tsawon lokacin da aka kwashe don sanin gaskiyar lamarin. Ina kara godiya a gareka bisa bani damar hidimtawa kasar nan karkashin mulkinka, lallai dama ce babba, wacce kuma ko kadan ba zan dauke ta da wasa ba.

A matsayina na yar Nigeria wacce ta kafu akan ci gaba, na ji dadin yadda kake kokari wajen ganin an samu ci gaba a kasar nan.

Ina so ka sani, a har kullum, ina yi maka fatan alkairi da samun nasara akan kudurorin da ka sanya a gabanka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel