Yaki da Barayi ba abu bane mai sauki a Najeriya – Inji Shugaba Buhari

Yaki da Barayi ba abu bane mai sauki a Najeriya – Inji Shugaba Buhari

Mun samu labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda Gwamnatin sa ke gwagwarmaya da wadanda su ka saci dukiyar kasar nan inda yace abu ne mai matukar wahala.

Yaki da Barayi ba abu bane mai sauki a Najeriya – Inji Shugaba Buhari
Gwamnatin Buhari na kokarin ginawa jama’a gidajen zama a Najeriya
Asali: Depositphotos

A jiya ne Shugaban kasar ya bayyana irin rawar da Gwamnati sa ta ke yi wajen ganin abubuwan sun dawo daidai a kasar nan. Shugaba Buhari yace sun yi kokari wajen gina sababbin tituna da kuma tada wadanda aka manta da su.

Shugaban kasar ya kuma ce Gwamnatin sa ba tayi kasa a gwiwa wajen babbako da hanyoyin jirgin kasa ba. Buhari ya kuma bayyana cewa yana bakin kokarin wajen gyara titunan jiragen sama da kuma tashoshin ruwan da ke Najeriya.

KU KARANTA: An bankado satar kudin makamai da aka yi a Najeriya

Sai dai Shugaba Buhari ya nuna cewa yaki da barayin kasar nan sam bai zuwa da sauki. Shugaban kasar yace barayin Najeriya na bakin kokarin su na kawo masa matsala wajen wannan aiki da ya sa gaba na kawar da barna a fadin kasar.

Duk da kalubalen da ake samu dai Shugaban kasar yace Gwamnatin sa za ta cigaba da bakin kokarin ta wajen ganin Najeriya ta gyaru. Buhari ya bayyana cewa tsarin asusun bai-daya na TSA yana cikin manyan nasarorin da su ka samu.

A jawabin da Shugaban kasar yayi a shafukan sa na sadarwa ya tabbatar da cewa yanzu an daina yin awon gaba da kudin Gwamnati kamar yadda aka saba a baya. Buhari ya kuma ce an samu nasara wajen harkar noma a Gwamnatin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel