Da duminsa: Dakarun soji sun yiwa 'yan Boko Haram da suka kai masu hari kisan kiyashi, hotuna
Rundunar sojin najeriya ta 145 dake aikin tabbatar da zaman lafiya a Maiduguri (Ofireshon Lafiya Dole) sun yiwa wasu mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai masu hari a sansaninsu kisan kiyashi. Mayakan na kungiyar Boko Haram sun kai harin ne jiya, Laraba, 12 ga watan Satumba , 2018.
Dakarun sojin sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram da dama tare da lalata makamansu masu yawa. Yanzu haka dakarun sojin na cigaba da farautar ragowar ‘yan mayakan Boko Haram din da suka tsere, kamar yadda Birgediya Texas Chukwu, darektan hulda da jama’a na hukumar soji, ya sanar ta shafin Kanal Sani Kukasheka Usman.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng