'Yan bindiga sun yiwa mutane kisan kiyashi a Zamfara

'Yan bindiga sun yiwa mutane kisan kiyashi a Zamfara

- Wasu 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Badarawa da ke jihar Zamfara

- 'Yan bindigan sun hallaka mutane 13 tare da raunana wasu adadin mutane masu yawa

- Jami'an 'yan sanda da sojojin Najeriya sun hallara kauyen domin bin sahun 'yan bindigan

'Yan bindiga sun kashe mutane 13 tare da raunata wasu da dama a wata hari da suka kai a kauyen Badarawa da ke karamar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun far ma kauyen ne da safiyar jiya yau Alhamis inda suka rika harbin dukkan wanda suka hadu dashi kuma daga baya suka rika bi gidajen mutane daukan abinda suke so.

'Yan bindiga sun yiwa mutane kisan kiyashi a Zamfara
'Yan bindiga sun yiwa mutane kisan kiyashi a Zamfara
Asali: Twitter

Duk da cewa Rundunar 'yan sanda na jihar Zamfara ta ce mutane shida kawai aka kashe a harin, wata kwakwarar majiya daga kauyen ta ce mutane 13 ne suka rasu sakamakon harin.

DUBA WANNAN: Babban malamin Islama na son a rage albashin 'yan siyasa

Kakakin Rundunar 'yan sandan jihar, Mohammad Shehu, ya tabbatar da afkuwar harin ga majiyar Legit.ng amma ya ce mutane shida aka kashe a harin.

'Yan bindiga sun yiwa mutane kisan kiyashi a Zamfara
'Yan bindiga sun yiwa mutane kisan kiyashi a Zamfara
Asali: Twitter

"Rahotannin da muka samu sun nuna cewa mutane shida aka kashe a harin, yayin da wasu 10 suka sami munanan raunuka.

"Bayan an sanar da mu abinda ke faruwa, mun garzaya kauyen cikin gagagwa tare da sojojin Najeriya. Muna bin sahun 'yan bindigan a daji domin gano inda suke buya.

"Mun baza jami'an sintiri a kauyen a yanzu kuma mutane sun fara cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba," inji mataimakin sufritanda, Shehu.

Tuni dai aka yi jana'izar mutane da suka riga mu gidan gaskiya a harin na 'yan ta'adda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel