2019: Kungiyoyi 5 sun sayawa El-Rufa’i fam din takarar gwamna
- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya karbi fam din takarar gwamna da wasu kungiyoyi biyar suka hada suka saya masa
- El-Rufa’i ya ce hankalinsa ya tashi bayan jam’iyya ta fitar da farashin fam din takara tare da bayyana cewar bashi da miliyan N20m a asusun sa
- Gwamnan ya ce asusun banki daya gare shi kuma kudin dake ciki bai kai adadin kudin da zasu saya masa fam din takarar gwamna ba
Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kan su (IPMAN), kungiyar direbobi masu dakon man fetur (PTD), kungiyar direbobi (NARTO) da Karin wasu kungiyoyi biyu sun sayawa gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i, fam din takara.
Da yake karbar fam din takarar a jiya, Litinin, El-Rufa’i, ya yiwa kungiyoyin godiya tare da shiada masu cewar sun sauke masa nauyi domin ba kankanin tashin hankali ya shiga ba bayan jam’iyyar APC ta fitar da farashin fam din takara.
“Na shiga damuwa bayan jam’iyyar APC ta fitar da farshin fam saboda maganar gaskiya bani da miliyan N20m a asusuna guda daya tal da nake da shi a bankin GT.
DUBA WANNAN: 2019: Surukin Buhari ya sayi fam din takarar gwamna a APC
“A matsayinmu na gwamnoni, mun fara tattauna yadda zamu hada kudi domin sayawa Buhari fam amma bayan wata kungiya ta riga mu saya masa sai na fara tunanin waye zai saya min nawa fam din domin bani da zunzurutun kudin da suka kai miliyan N20m,” in ji El-Rufa’i.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng