Allah ya yiwa babban malamin Izala a Kaduna rasuwa

Allah ya yiwa babban malamin Izala a Kaduna rasuwa

Allah ya yiwa daya daga cikin malaman izala kuma limamin masallacin juma’a na NNDPC dake garin Kaduna, Sheikh Abubakar Baban Tune, rasuwa a yau, Lahadi, a asibitin shika na garin Zaria.

An yi jana’zar malamin da Magriba a masallacin unguwar Low Cost dake garin Zaria, kamar yadda fitaccen malami, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya sanar a shafinsa na Facebook. •

Muna addu'ah Allah Ta'ala Ya Jikan Malamin mu Sheikh Abubakar Baban Tune (Babban Limamin Masallacin Juma'ah na NNPC Kaduna) Ya rasu Yau Litinin 30 Dhul Hajj, 1439H, 10 Sept, 2018 a Asibitin Shika, Zaria.

Allah ya yiwa babban malamin Izala a Kaduna rasuwa
Marigayi Sgheikh Abubakar
Asali: Facebook

Za'ayi Jana'iza da Magriba a Masallacin Low coast dake Zaria.

Allah Ta'ala Ya Jikansa da Rahama Ya gafarta masa Yasa Mutuwa ta zama Hutu a gare shi, Ya karbi ayyukan sa na alkhairi, na kuskure Kuma Allah Ya yafe, Allah yasa tamu tayi kyau bayan tasu. Amin,” kamar yadda Sheikh Gumi ya rubuta a sahafinsa na Facebook

DUBA WANNAN: 2019: Tsohon IG, Sulaiman Abba, ya yanki fam din takarar sanata a APC

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya halarci bikin bude wata makarantar Islamiyya a unguwar Kaura dake garin Zaria, a jiya Lahadi.

Tsohon jakadan Najeriya a kasar Ingila, Dalhatu Sarki Tafida, ne ya gayyaci gwamna El-Rufa'i bikin bude makarantar da aka gina domin tunawa da marigayi Malam Abubakar Magatakarda Tafida( Baba Maidoki).

Makarantar zata bawa ilimin mata muhimmanci, a bangaren addinin Islama da na boko.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel