Abinda ya farraka ni da Shekarau – Takai

Abinda ya farraka ni da Shekarau – Takai

Malam Salihu Sagir Takai, tsohon kwamishina kuma na hannun damar tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya ce sun yi hannun riga a siyasance da tsohon maigidan nasa.

Takai da Shekarau sun dade tare suna gwagwamarya a siyasa.

Takai na daga cikin kwamishinoni masu fada-a-ji a gwamnatin Kano lokacin da Shekarau ke gwamna.

Shekarau ne ya fara tsayar da Takai takarar gwamana a Kano a shekarar 2011 bayan zangonsa yak are kafin ya kara mara masa baya a shekarar 2015.

Waka bakin mai ita: Dalilin da yasa na raba jiha da Shekarau - Takai
Waka bakin mai ita: Dalilin da yasa na raba jiha da Shekarau - Takai
Asali: Twitter

Sai dai a lokacin da ake tunanin cewar Takai zai kasance tare da Shekarau bayan ya canja sheka zuwa APC a ranar Juma’a, sai gas hi Takai ya bayyana cewar zai cigaba da zama a jam’iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamna ya sayi fam din takara daga gidan yari

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau,ya bayyana cewar rashin adalcin da uwar jam’iyyar PDP ta nuna masa ne silar komawarsa jam’iyyar APC.

Shekarau ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi ga dubban magoya bayansa daga kananan hukumomin Kano 44 a wurin gangamin taron bikin karbarsa a jam’iyyar APC da aka yi a gidansa dake unguwar Mundubawa.

A karshe, Malam Ibrahim Shekarau, ya yanki katin shaidar zama dan APC a ofishin jam'iyyar dake mazabar sa ta Giginyu a karamar hukumar Nasara dake Kano a jiya, Lahadi.

Sai dai Malam Takai y ace rashin gamsuwa da dalilan da Shekarau ya bayar ne ya saka shi kin komawa APC tare da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel