Gasar shan giya: Dalibin jami'a ya kare a gadon asibiti bayan lashe gasar N5,000

Gasar shan giya: Dalibin jami'a ya kare a gadon asibiti bayan lashe gasar N5,000

Rayuwar wani dalibi, Hassan Faruk, dake karatu a jami’ar koyon noma dake garin Abeokuta a jihar Ogun, ta shiga hatsari bayan ya shiga gasar shan giya da wani abokinsa.

Faruk, dalibi dake shekarar sa ta uku a jami’a, ya fadi sumamme bayan bayan ya yiwa giya mai zafi shan ruwa da aka fi sani da kaakaki.

Yanzu haka an garzaya da matashin asibiti domin ceto rayuwarsa, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Gasar shan giya: Dalibin jami'a ya kare a gadon asibiti bayan lashe gasar N5,000
Dalibin jami'a ya kare a gadon asibiti bayan lashe gasar shan giya
Asali: Facebook

Ko a daren jiya Legit.ng ta kawo maku labara mai nasaba da wannan in da dan sarkin Musulmi mai suna Amir ya debi mota da gudu misalin karfe 12 na rana wajen filin jirgin saman jihar Sokoto.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta bayar da hutun sabuwar shekarar Musulunci

Ya kasance a buge tare da wani abokinsa mai suna Khalifa Maccido da wata yarinya da suka kawo daga jihar Kaduna.

Idanuwan shaida sun bayyana cewa Amir na buge lokacin da yake tuki kuma an samu kwalban Benelyn Codeine a motar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng