El-Rufa’i ya halarci bikin bude Islamiyya da jigo a PDP ya gina a Zaria, hotuna

El-Rufa’i ya halarci bikin bude Islamiyya da jigo a PDP ya gina a Zaria, hotuna

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya halarci bikin bude wata makarantar Islamiyya a unguwar Kaura dake garin Zaria, a jiya Lahadi.

Tsohon jakadan Najeriya a kasar Ingila, Dalhatu Sarki Tafida, ne ya gayyaci gwamna El-Rufa'i bikin bude makarantar da aka gina domin tunawa da marigayi Malam Abubakar Magatakarda Tafida( Baba Maidoki).

Makarantar zata bawa ilimin mata muhimmanci, a bangaren addinin Islama da na boko.

El-Rufa’i ya halarci bikin bude Islamiyya da jigo a PDP ya gina a Zaria, hotuna
El-Rufa’i na gaisawa da sarkin Musulmi mai alfarma, Sa'ad Abubakar II.
Asali: Facebook

El-Rufa’i ya halarci bikin bude Islamiyya da jigo a PDP ya gina a Zaria, hotuna
Sarkin Muslmi yayin kaddamar da makarantar Islamiyya
Asali: Facebook

Mai alfarma sarkin musulmi, Abubakar Sa’ad II, ne ya kasance bako na musamman a wurin taron bude makarantar.

Wanda ya gina makarantar, Dalhatu Sarki Tafida, jigo ne a jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Manyan Najeriya sun halarci bikin diyar ministan Buhari

Ya taba zama Sanata a PDP kafin daga bisani gwamnatin jam'iyyar ta tura shi kasar Ingila a matsayin jakadan Najeriya.

El-Rufa’i ya halarci bikin bude Islamiyya da jigo a PDP ya gina a Zaria, hotuna
El-Rufa’i ya halarci bikin bude Islamiyya a Zaria
Asali: Facebook

El-Rufa’i ya halarci bikin bude Islamiyya da jigo a PDP ya gina a Zaria, hotuna
El-Rufa’i ya halarci bikin bude Islamiyya a Zaria
Asali: Facebook

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel