'Yan siyasan Kano da suka sauya sheka zuwa APC tare da Mallam Ibrahim Shekarau

'Yan siyasan Kano da suka sauya sheka zuwa APC tare da Mallam Ibrahim Shekarau

- A yau Asabar ne tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shakarau, ya sanar da komawarsa jam'iyyar APC

- Shekarau ya fice daga PDP ne saboda rashin adalci da ya ce anyi masa a jam'iyyar kuma uwar jam'iyyar taki daukan mataki a kai

- Duk da cewa bai tursasa na kusa dashi sauya sheka ba, an samu mafi yawancinsu da suka sauya shekan tare dashi

A yau, Asabar 9 ga watan Satumba ne tsohon gwaman jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya tabbatar da komawarsa zuwa jam'iyyar APC, hakan yasa masu fashin bakin siyasa su kayi fashin baki kan magoya bayansa da zasu bi shi zuwa APC.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Mallam Shekarau ya shaidawa magoya bayansa cewa ya yanke shawara komawa APC ne bayan ya yi kokarin kwato hakkinsa da aka tauye amma hakan ya ci tura.

'Yan siyasan Kano da suka sauya sheka zuwa APC tare da Mallam Ibrahim Shekarau
'Yan siyasan Kano da suka sauya sheka zuwa APC tare da Mallam Ibrahim Shekarau
Asali: Twitter

"Ciyaman din PDP na kasa, Uche Secondus ya dena amsa waya ta, haka shima Aminu Wali da Bello Hayatu. Munyi iya kokarinmu domin mu kwato hakkinmu amma uwar jam'iyya ta nuna halin ko in kula a garemu," inji Shekarau.

DUBA WANNAN: Daya daga cikin masu son takarar shugaban kasa a PDP ya janye

Rahoton ya cigaba da cewa Shekarau ya kira taron magoya bayansa inda ya sanar dasu niyyarsa na komawa APC kana ya bawa magoya bayansa zabi na sauya shekar tare dashi ko kuma suyi zamansu a PDP.

Majiyar Legit.ng ta ce mafi yawancin wadanda suka hallarci taron sun yanke shawara bin Shekarau zuwa APC amma tsohon kwamishinansa kuma amininsa, Salihu Sagir Takai ya ce zai zauna a PDP.

Farouq Iya, tsohon Ciyaman din PDP na jihar Kano kuma shugaban yakin neman zaben Takai, shima ya ce zai cigaba da zama a PDP.

Wasu daga cikin sananun mutanen da suka sauya sheka tare da Shekarau sun hada da Senata Mohammed Bello, tsaffin kwamishinoni, Garba Yusuf, Sarki Labaran da Musa Shanono.

Saura sun hada da Umar Mustapha Maimansaleta, Bello Sani Gwarzo, Nasir Sorondinki, Bashir Ishaq Bashir, Ahmed Aruwa, Mamuda Sani Madakingini, Nasiru Madana Fagge da Shehu Isa Direba.

Cikin shugabanin jam'iyya kuma wadanda suka bi Shekarau sune, Ibrahim Mai Atampa (Mataimakin Ciyaman, Kano ta Kudu) Shehu Na’Allah Kura (Mataimakin Ciyaman, Kano ta Tsakiya), Ibrahim KT (Mataimakin Ciyaman), Auwal Danzabuwa (Sakataren jiha na PDP), Usman KK (Shugaban Matasa) da Riga Yakasai (Shugaban Mata).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel