Hotunan artabun da Soji su kayi da Boko Haram yayin da suka ceto mutane 21 da aka sace
A yau, Juma'a, Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da cewa tayi nasarar ceto wasu matafiya 21 da mayakan Boko Haram su sace a ranar Laraba.
Dakarun sojin sun kashe mayakan Boko Haram hudu a artabun da su kayi wajen ceto matafiyan kamar yadda hukumar sojin ta sanar.
A ranar Talata da ta gabata, mayakan kungiyar Boko Haram sunyi kwantar bauna inda suka tare wata motar fasinjoji a hanyar Gwoza-Pulka da Warabe inda suka sace matafiyan.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Fasinjoji sun shiga zullumi bayan lalacewan jirgin kasa a garin da ake yawan sace mutane

Asali: Twitter
Hukumar Sojin ta ce 'yan bangaren Abubakar Shekau ne da ke buya a dajin Gwoza suka sace mutanen.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Direktan sashin hulda da jama'a na sojin, Texas Chukwu, ya ce dakarun sojin sun kai sumamen ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba inda sojojin suka kai farmaki a mabuyar 'yan Boko Haram.

Asali: Twitter
Chukwu ya ce dakarun sojin sun ceto mata shida, yara 11 da maza hudu kuma a halin yanzu suna asibitin sojoji inda ake basu kulawa ta musamman.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng