Mazauna birnin Abuja sun firgita yayin da aka yi girgizan kasa da daddare

Mazauna birnin Abuja sun firgita yayin da aka yi girgizan kasa da daddare

Jama’a su shiga halin firgici da tashin hankali yayin da aka samu wata karamar girgizan kasa na tsawon dakika 30 zuwa 40 a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar This Day ta bayyana a cikin rahotonta.

Legit.ng ta kalato cewa wannan lamari ya faru ne a daren Laraba, 5 ga watan Satumba, inda mazauna unguwannin Mpape da Maiatama duk sun shaida da kuma tabbatar da faruwar lamarin.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta yi watsi da tsarin kato bayan kato a zaben fidda gwani

Wata mata da ta shaida faruwar girgizan mai suna Fatima Ahmedu ta bayyana lamarin a matsayin abin firgitarwa, inda tace gidanta gaba daya rawa ya dinga yi a lokacin da girgizan ya auku, ganin haka yasa ta fita gida da gudu.

Mazauna birin Abuja sun firgita yayin da aka yi girgizan kasa da daddare
Wani Titi
Asali: Depositphotos

Sai dai hukumar bada agajin gaggawa ta Abuja ta danganta faruwar lamarin da wasu sauyi da ake samu a cikin kasa, wanda ake kiransa da suna ‘Seismic’ a turance, kamar yadda shugaban hukumar Abbas G Idriss ya bayyana, haka zalika yace fashe fashen manyan duwatsu ka iya janyo wannan girgizan.

“Jama’a na ta kiranmu a waya sakamakon girgizan kasan da aka samu a unguwannin Mpape da Maitama, muna sanar da mutane cewa musabbabin wannan lamari shine wani sauyi da ake samu a cikin kasa, wanda yake sako wasu sinadarai dake girgiza kasar da muke kanta.” Inji shi.

Da wannan ne shugaban hukumar yayi kira ga jama’a dasu kwantar da hankulansu, inda yace abu ne mai wuya a samu girgizan kasa a Abuja da ma Najeriya gaba daya, sakamakon kasar Najeriya ba ta cikin yankunan kasashen dake girgiza.

Daga karshe hukumar ta bayyana ma jama’a dabarun daya kamata su yi idan lamarin ya sake faruwa, inda yace jama’a su shiga dakin da babu kaya dayawa, su tsugunna, su boye a kasan teburi, sa’annan su rike shi gam gam. Sa’annan ta shawarci wadanda lamarin ya rutsa dasu a waje da su kauce ma gidaje, bishiyu da wayoyin wutar lantarki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel