Lalacewa: Miji ya cizge leben matar sa yayin da suke dakuwa

Lalacewa: Miji ya cizge leben matar sa yayin da suke dakuwa

Wani mutumin kasar Kenya, David Munga, ya shiga hannun hukuma bayan ya cizge leben matar sa na kasa yayin da suke fada.

A cewar wani gidan talabijin na kasar Kenya, Citizen TV, Mungai na yawan dukan matar sa, Anne Waireri, tare da ji mata rauni a wasu lokutan.

Mungai da Anne sun yi wani fada ne a ranar 29 ga watan Agusta, ranar da ya cizge mata lebenta na kasa.

Makwabtan Mungai ne suka tona asirin inda yake boye bayan ya jiwa matar tasa ciwo.

Lalacewa: Miji ya cizge leben matar sa yayin da suke dakuwa
Matar da miji ya cizgewa lebe
Asali: Depositphotos

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar wasu mata guda 6 dake takarar kujerar shugaban kasa sun bayyana dalilinsu na son karbar mulkin Najeriya daga shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: 2019: Zan inganta noman tabar wiwi idan na zama shugaban kasa - Dan takara

Matan 6 – Farfesa Olufunmilayo Adesanya-Davis, Dakta Oluremi Comfort Sonaiya, Dakta Elishama Rosemary Ideh, Adeline Iwuagwu-Emihe, Eunice Atuejide da Princess Oyenike Roberts – sun bukaci masu zabe su bawa mace dama domin kawo canji nan gaskiya a Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar matan na wakiltar kasha 60% na dukkan ‘yan takarar dake burin ganin sun karbi mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel