Siyasar Kano sai Kano: Akwai yiwuwar Shekarau ya samu mukami idan ya koma APC
Yanzu haka dai ana ta kishin-kishin din cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau yana shirin ya koma Jam’iyyar APC mai mulki. Mun kawo abubuwan da ka iya faruwa idan hakan ta tabbata.

Asali: Twitter
1. Kujerar Sanatan Kano ta tsakiya
Akwai yiwuwar APC ta nemi ba tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2019. Sai dai yanzu hakan wasu sun yi nisa a APC wajen wannan shiri kuma Shekarau din na iya samu idan har Kwankwaso su ka tsaida wani ‘Dan takaran kujerar a PDP.
2. Minista a Gwamnatin Shugaba Buhari
Ba mamaki kuma Gwamnatin Tarayya tayi wa tsohon Gwamnan tayin kujerar Minista. A karshen lokacin mulkin PDP, an nada Shekarau a matsayin Ministan ilmi na wani kankanin lokaci kafin zuwa Gwamnatin Buhari. Shekarau dai yayi takara da Buhari a 2011 kafin a kafa Jam’iyyar APC.
KU KARANTA: PDP ta sake yi wa Shugabancin PDP garambawul a Kano
3. Kujerar Mataimakin Gwamnaan Kano
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje zai iya yi wa tsohon Gwamnan tayin kujerar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ga mutanen sa tare da yi masu alkawarin damawa da su a Gwamnatin Jihar. Yanzu haka dai Mataimakin Ganduje ya ajiye aiki ya bi tsohon Gwamna Kwankwaso.
Dazu kun ji cewa babban ‘Dan takarar PDP Rabiu Kwankwaso yayi wani babban bako daga Kasar Turai. Babban Jakadan Birtaniya a Najeriya Paul Arkwright ne ya ziyarci Rabiu Kwankwaso a gidan sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng