Babu gidan da babu dan Kwankwasiyya a Arewacin Najeriya – Kwankwaso yayi baki

Babu gidan da babu dan Kwankwasiyya a Arewacin Najeriya – Kwankwaso yayi baki

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi ma jam’iyyar PDP barazana game da yawan magoya bayansa dake yankin Arewacin Najeriya, da aka fi sani da ‘Yan Kwankwasiyya.’.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kwankwaso yayi wannan baki ne a yayin daya yanki takardar takarar shugaban kasa a babban ofishin jam’iyyar PDP, inda yace akwai dan Kwankwasiyya a kowanne gida dake Arewacin Najeriya, karanci kenan.

KU KARANTA: Da dumi dumi: APC ta fitar da farashin tsayawa takarar mukamai daban da

“Mun yi aiki tukuru muka samar da tafiyar Kwankwasiyya, ina fada maka a yau abin mamaki ne ace an samu gidan da babu dan Kwankwasiyya a kafatanin yankin Arewa gaba daya kwata, ya kamata a sani cewa yayan Kwankwasiyya suna da da’a, ladabi da biyayya, kuma muna da burin gyara Najeriya.

Babu gidan da babu dan Kwankwasiyya a Arewacin Najeriya – Kwankwaso yayi baki
Kwankwaso
Asali: Depositphotos

“Na tabbata kaga Kwankwasawan da suka halarci taron kaddamar da takarata, inda matasa maza da mata suka daga dukkanin sassan Arewa suka fito, wasu ma motar Tirela suka bi, duk da cewa ana damuna, amma basu damu ba, ko a jikinsu.

“Murna ma suke yi, saboda bukatarsu a samu kyakkyawan shugabanci a Najeriya, kuma nima ina farin cikin samun jajirtattun matasa kamarsu suna mara min baya, ba kudi suke nema ba, mutane ne da suke da burin ganin sun kada kuri’u, kuma sun kare kuri’unsu, wannan shine ma’anar Kwankwasiyya, kuma da wannan nafi karfin sauran masu takarar shugaban kasa a PDP.” Inji shi.

Jam’iyyar PDP ta sanar da fara sayar da takardar takarar shugabancin kasar nan ga masu sha’awar yin haka daga cikin yayanta, inda ta sanya shi akan kudi naira miliyan goma sha biyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel