Ladan noma: Wani manomi ya dauki alwashin sayan ma Buhari takardar takara

Ladan noma: Wani manomi ya dauki alwashin sayan ma Buhari takardar takara

Wani manomi da cikin manoman da suka amfana da tsare tsare harkar noma da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bullo dasu ya bayyana bukatarsa ta yankan ma shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar tsayawa takara na jam’iyyar APC.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin jam’iyyar APC reshen jahar Legas, Joe Igbokwe ne ya sanar da haka a shafinsa, inda ya bayyana sunan wannan manomi a matsayin Kabiru Ishaq Sa’idu.

KU KARANTA: Rai bakon duniya: Yadda wata Kada ta yi kalaci da wata Uwa da jariryarta

Ladan noma: Wani manomi ya dauki alwashin sayan ma Buhari takardar takara
Malam Kabiru
Asali: Facebook

Malam Kabiru yace: “A matsayina na manomi, kuma wanda ya kirkiri kungiyar manoman ‘Northern Avengers’ zai taimaka ma bukatar shugaban kasa na sake komawa kujerarsa a karo na biyu, don haka zan bada naira miliyan 5, taimakona don sayan takardar takararsa.

“Zan yi haka ne don nuna godiyata ga Baba Buhari, bisa kokarin na baiwa manoma kwarin gwiwa, tare da nuna ma yan Najeriya cewa harkar noma itace hanyar samun arziki cikin sauki, tare da zama da kafarka.” Inji Kabiru.

Malam Kabiru ya kirkiri Northern Avengers ne don mayar da martani da tsagerun Neja Delta da suka kafa wata kungiya mai suna Niger Delta Avengers, suna fasa bututun mai, suna kashe jami’an tsaro tare da garkuwa da mutane.

A wani labarin kuma, jam’iyyar APC ta fitar da sahihin farashin shiga takara a karkashin inuwarta, inda ta sanya naira miliyan 40 ga masu sha’awar takarar shugaban kasa, da miliyan 20 ga masu takarar gwamna

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel