Wani Matashi ya sheme Mahaifiyarsa da Katako a jihar Legas

Wani Matashi ya sheme Mahaifiyarsa da Katako a jihar Legas

Mun samu cewa wata Kotun Majistire dake zamanta a garin Ebute Meta na jihar Legas, ta bayar da umarnin garkame wani matashi mai shekaru 25 a gidan kaso, Taiwo Akinola, bisa aikata laifin hali na 'dan yau inda ya sheme Mahaifiyarsa da Katako har tsakiyar ka.

Ana zargin wannan Matashi da laifi na yunkurin kisan kai kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana.

Alkaliyar kotun, Mrs O. A Komlafe, ita ta bayar da umarni na garkame wanda ake zargi a gidan kaso na Ikoyi domin samun dama ta neman shawara daga cibiyar zartar da hukunci ta jihar dangane da wannan lamari.

Wani Matashi ya sheme Mahaifiyarsa da Katako a jihar Legas
Wani Matashi ya sheme Mahaifiyarsa da Katako a jihar Legas
Asali: Depositphotos

Jami'in dan sanda mai shigar da kara Kehinde Omisakin ya bayyanawa kotun cewa, Mista Akinola ya aikata wannan laifi ne da misalin karfe 8.00 na safiyar ranar 19 ga watan Agusta a gidansu mai lamba 2 dake layin Raji Ajanaku na unguwar Ayobo ta jihar Legas.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuwar Soji da wasu Mutane 9 a jihar Kebbi

Omisakin yake cewa, a yunkurin Omisakin na sheke mahifiyarsa, Iyabo Fawole, mai shekaru 68, ya yi amfani da wani jan katako inda ya sheme ta har tsakiyar ka, wanda wannan lamari ya ci karo da sashe na 230 cikin dokokin jihar.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Alkaliya Komlafe ta daga sauraron wannan kara zuwa ranar 8 ga watan Okotoba domin ci gaba da shari'a tare da yanke ma sa hukuncin da ya dace da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel