Dan takarar gwamna a jihar Saraki ya fita daga PDP, ya koma APC

Dan takarar gwamna a jihar Saraki ya fita daga PDP, ya koma APC

Mai neman PDP ta tsayar da shi takarar gwamna a jihar Kwara, Sunday Babalola, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar tare da tsallakwa zuwa jam’iyyar APC.

Injiniya Babalola, ya bayyana cewar ya fita daga PDP ne saboda ba zai iya zama a jam’iyya daya da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ba.

Da yake sanar da canjin shekarsa a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Babalola ya ce “na koma koma jam’iyyar APC tare da magoya baya na fiye da 20,00 da suka fito daga sassan jihar nan daban-daban.”

Sannan ya cigaba da cewa, “Saraki ya fita daga APC ne bayan duk kokarinsa na rusa jam’iyyar ya ci tura, hakan ya saka shi komawa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP domin samun dammar cigaba da cin karensa babu babbaka. Wannan ne ya saka na koma APC domin ba ta gudunmawar cigaba aiyukan gina kasa.”

Dan takarar gwamna a jihar Saraki ya fita daga PDP, ya koma APC
Saraki
Asali: Depositphotos

Ba zan iya zama jam’iyya daya da mutanen da basu da wani buri da ya wuce su hana cigaban jihar Kwara da mutanenta. A matsayina na dan takara kuma mai yin zabe, na yanke shawarar shiga jam’iyyar APC.”

DUBA WANNAN: Nayi nadamar rashin yiwa PDP wani muhimmin gata a 2003 - Atiku

Fiye da shekaru 45 kenan wasu ‘yan tsirarun mutane sun saka jihar Kwara a aljihunsu, sun jefa jama’a cikin fatara da talauci. Lokaci ya yi da zamu tashi tsaye domin ganin mun kwace ‘yancinmu da hakkinmu daga hannu irin wadannan mutane.”

A wani labarin mai alaka da wannan, tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Donald Duke, ya canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa SDP, jam’iyyar da yake son yin takarar shugaban kasa a cikinta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel