Bashin da kasar China za ta bayar ba alakakai bane, zamu iya biya - Buhari

Bashin da kasar China za ta bayar ba alakakai bane, zamu iya biya - Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya zata iya biyan basusukan da ta karba daga kasar China

- Shuagaban kasar ya lissafa wasu daga cikin ayyukan da aka gudanar karkashin yarjejeniyar ta FOCAC

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tsokaci kan bashin da Najeriya ta karba daga kasar China inda ya ce Najeriya za ta iya biyan bashin ba kamar yadda wasu ke ganin cewa bashin zai zama matsala ga Najeriya nan gaba.

Bashin da kasar China zata bayar da alakakai bane, zamu iya biya - Buhari
Bashin da kasar China zata bayar da alakakai bane, zamu iya biya - Buhari
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa tsakanin China - Afirka (FOCAC) a Beijing. Najeriya ta karbi bashin kimanin $5 biliyan cikin shekaru 3 da suka gabata inda aka rika amfani da kudaden wajen gudanar da ayyuka musamman a fanin gine-gine.

DUBA WANNAN: Ba zan sake takara ba, bayan wannan karon - Makarfi

A taron da aka gudanar tsakanin shugabanin Afirka da shugaba Xi Jinping na Chisa, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce: "Wadannan ayyukan gine-ginen masu muhimmanci sunyi dai-dai da tsarin farfado da tattalin arzikin mu. Kasar mu za ta iya biyan basusukan da ta karba a lokacin da ya dace."

Da yake lissafa ayyukan da Najeriya ta gudanar da kudaden da aka karba bashi karkashin FOCAC, shugaba Buhari ya bayar da misalin aikin layin dogo da aka kaddamar a babban birnin tarayya Abuja cikin watan Yulin shekarar 2018 wanda ya lashe a kalla $500miliyan.

Ya kuma kara da cewa akwai wasu ayyuka da dama da ake gudanarwa wanda suka hada da layin dogo daga Abuja zuwa Kano, aikin wutan lantarki na Zungeru da aikin samar da intanet na zamani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel