Da dumi dumi: APC ta fitar da farashin tsayawa takarar mukamai daban daban

Da dumi dumi: APC ta fitar da farashin tsayawa takarar mukamai daban daban

Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da sahihan farashin kudin yankan takardun tsayawa takarkaru daban daban a cikinta, wanda hakan ya kawo karshen jita jitan da ake yadawa game da wani farashi dake yawo a shafukan sadarwa ana cewa na jam’iyyar ne.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito wata majiya ta karkashin kasa daga cikin jam’iyyar ne ya tsegumta mata haka, inda ta kalato cewar uwar jam’iyyar zata fara sayar da takardun tsayawa takarar ne daga ranar Laraba, 5 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Yan bindiga sun farfado a hanyar Kaduna-Abuja, sun kashe mutane biyu

Da dumi dumi: APC ta fitar da farashin tsayawa takarar mukamai daban daban
Taron APC
Asali: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta ruwaito farashin shiga takarar mukaman siyasa daban daban kamar haka:

Takarar majalisar jaha: Naira dubu dari bakwai da hamsin (N750, 000)

Takarar majalisar wakilai: Naira miliyan Uku da dubu dari biyar (N3, 500, 000)

Takarar majalisar dattawa: Naira miliyan shida (N6, 000, 000)

Takarar gwamna: Naira miliyan ashirin (N20, 000, 000, 000)

Takarar shugaban kasa: Naira miliyan arba’in (N40, 000, 000)

Idan za’a tuna a cikin makon daya wuce ne aka dinga watsa wani farashi a shafukan yanar gizo dake cewa yan takarkarun kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC zasu sauke ma jam’iyyar zambar kudi naira miliyan 50 a matsayin kudin yankan takardar tsayawa takara, sai dai ba cinya ba, kafar baya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel