Irin mu ne cikakkun ‘Yan siyasa a Kasar nan inji tsohon Gwamna Kwankwaso

Irin mu ne cikakkun ‘Yan siyasa a Kasar nan inji tsohon Gwamna Kwankwaso

Mun samu labari cewa Sanatan Jihar Kano ta tsakiya watau Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yayi takarar siyasa fiye da sau 10 daga fara siyasar sa zuwa yanzu a Najeriya.

Irin mu ne cikakkun ‘Yan siyasa a Kasar nan inji tsohon Gwamna Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso yace sai wanda ya fadi zabe ya san siyasa
Asali: Depositphotos

‘Dan takarar Shugaban kasar ya bayyana cewa sai wanda ya saba fadi zabe ne ya san harkar siyasa a Najeriya. A cewar tsohon Gwamnan na Kano Kwankwaso, wanda bai taba fitowa takara an tika shi da kasa bai san menene siyasa ba.

Kwankwaso yayi wannan jawabi ne ga Legit.ng lokacin da aka hana sa amfani da farfajiyar Eagles Square domin kaddamar da shirin tsayawar sa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP inda yace an nuna masa karfin iko ne.

Injiniya Rabiu Kwankwaso yake cewa kafin zaben 2015 lokacin yana Jam’iyyar adawa, Gwamnati ta hana sa Eagle Square amma kuma an bar sa yayi amfani da wani filin fareti. Kwankwaso yace irin wannan kama-karya ce ake gudu a Kasar.

KU KARANTA: Ina da Digiri fiye da 10 don haka zan iya gyara Najeriya - Dankwambo

Wannan karan kuwa sam Gwamnati ba ta bar 'Dan siyasar yayi amfani da wani babban fili domin yin taron na sa ba. Kwankaso yake cewa daga fara siyasar sa, yayi takara sau 15 inda ya sha kasa sau 2 kacal a 2013 da kuma 2014.

Tsohon Gwamnan ya sha kasa a 2003 lokacin da ya nemi ya zarce a kan kujerar Gwamna a 2003. Bayan nan kuma Injiniya Kwankwaso ya fadi zaben fitar da gwanin Shugaban kasa na APC da aka yi a 2014 wanda yace yana alfahari da faduwar.

A shekarar 1992 ne aka zabi Rabiu MusaKwankwaso a matsayin ‘Dan Majalisar Wakilai na Tarayya. Haka kuma babban ‘Dan siyasar ya taba yin Ministan tsaro a 2003. Injiniya Kwankwaso ya zama Sanata ne bayan ya gama Gwamna a Kano a 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel