Ziyarar Buhari: Najeriya da China sun saka hannu a kan wasu aiyuka na $328m

Ziyarar Buhari: Najeriya da China sun saka hannu a kan wasu aiyuka na $328m

- A ranar Juma'a ne shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa China domin wata ziyarar aiki

- shugaba Buhari zai shafe kwanaki 6 a kasar ta China

-. A yayin ziyarar, shugaba Buhari zai saka hannu wasu aiyuka na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Najeriya zuwa kasar China a wata ziyarar aiki ta kwanaki 6.

Shugaba Buhari ya isa birnin Beijing na kasar China da misalin 9:00 (lokacin Najeriya) kuma ya samu tarbar girma daga manyan jami'an gwamnatin kasar da suka hada da jakadan China a Najeriya, Dakta Zhou Pingjian.

Ziyarar Buhari: Najeriya da China sun saka hannu a kan wasu aiyuka na $328m
Ziyarar Buhari a China
Asali: Twitter

Yayin ziyarar tasa, shugaba Buhari da takwaransa na kasar China, Xi Jinpin, zasu saka hannu a kan wani aikin bunkasa fasahar sarrafa bayanai ta zamani (ICT) da zai lashe Dalar Amurka $328.

DUBA WANNAN: Karuwan Najeriya sun yi watsi da Buhari, sun goyi bayan Saraki

Kazalika shugabannin biyu zasu saka hannu a kan wata yarjejeniyar bunkasa harkokin kasuwanci kamar yadda shugaban kasar China, Xi Jinpin, ya bukaci a yi tun shekarar 2013.

Mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Malam Garba Shehu, ya ce jami'an gwamnatin Najeriya tare da takwarorinsu na kasar China zasu saka hannu kan wasu yarjejeniya da suka kai a kalla 25 a bangarori daban-daban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel