Tafiyar Buhari 'Kasar Sin wata kitimurmura ce ta ƙulla maguɗin Zaɓe da tsige Saraki - Frank

Tafiyar Buhari 'Kasar Sin wata kitimurmura ce ta ƙulla maguɗin Zaɓe da tsige Saraki - Frank

A ranar Juma'ar da ta gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bankwana da birnin Abuja zuwa kasar Sin domin halartar taron hadin kan kasar da kuma nahiyyar Afirka karo na bakwai da za a gudanar kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, tsohon kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Timi Frank, ya bayyana wannan tafiya ta shugaba Buhari a matsayin wata kitimurmura ta ƙulla maguɗin babban zaɓe na 2019 gami da sabunta tuggu na tsige shugaban Majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.

Cikin sanarwar da ya bayyana a babban birnin kasar nan na tarayya, Frank yake cewa shugaba Buhari ya sake bayyana matsayar sa karara ta hamayya da mambobin sauran jam'iyyun adawa sakamakon tawagar sa da ta kunshi jiga-jigan gwamnati na jam'iyyar APC kadai.

Frank ya yi babatu da cewa ya kamata tawagar shugaba Buhari ta kunshi fitattun 'yan kasuwa da suka cancanci halartar wannan babban taro ba tare da la'akari da akidun su ta fuskar siyasa ba.

Shugaba Buhari yayin tafiyarsa 'Kasar Sin tare da iyalansa
Shugaba Buhari yayin tafiyarsa 'Kasar Sin tare da iyalansa
Asali: Twitter

Legit.ng ta ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta bayyana sunayen gwamnonin APC, Sanatoci da kuma kusoshin gwamnatin dake cikin tawagar ta shugaban kasa da suka hadar da, Gwamna Muhammad Abubakar, Akinwunmi Ambode, Muhammad Badaru Abubakar da kuma Rochas Anayo Okorocha na jihohin Bauchi, Legas, Jigawa da kuma Imo.

Tawagar ta kunshi Sanatocin APC da suka hadar; Abdullahi Adamu, George Akume, Godswill Akpabio da Aliyu Makko masu wakiltar jihohin Nasarawa, Benuwe, Akwa Ibom da kuma Sakkwato.

Kazalika tawagar ta shugaba Buhari ta kunshi Ministocin sa da suka hadar da; Ministan harkokin kasashen ketare; Geofferey Onyeama, Ministan Sufuri; Rotimi Amaechi, Ministan makamashi ayyuka da gidaje; Babatunde Fashola, Ministan Birnin tarayya; Muhammad Bello da Ministan Masana'antu, kasuwanci da hannun jari; Okechukwu Enelemah.

Sauran Ministocin sun hadar da; Ministan ruwa; Suleiman Adamu, Ministan kasafi da tsare-tsaren kasa; Udoma Udo Udoma, karamin ministan man fetur da ma'adanan sa; Ibe Kachikwu da kuma Karamin ministan sufuri na jiragen sama; Hadi Srika.

Tawagar ta kuma kunshin kusoshin gwamnati a suka hadar da; mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa; Babagana Monguno, shugaban hukumar NIA; Ahmed Abubakar da kuma shugaban kamfanin man fetur na kasa; Maikanti Baru.

KARANTA KUMA: Matar Gwamna Abubakar ta sha alwashin yaƙar ta'ammali da muggan ƙwayoyi a jihar Bauchi

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon kakakin jam'iyyar ya kausasa harshe kan tawagar shugaba Buhari sakamakon rashin gaurayata da mambobin jam'iyyun adawa wanda a cewar sa hakan shi zai tabbatar da kwararar romo na dimokuradiyya a kasar nan.

Ko shakka babu Frank a ranar Juma'ar da ta gabata ya yi hasashen cewa, wannan tafiya ta shugaban kasa wani ƙulli ne na shirya maguɗin zaɓe da kuma kitimurmura ta sauya shugabanci a majalisar dattawa.

Duk da cewa a baya shugaba Buhari ya gauraya tawagar sa ta tafiye-tafiye da mambobi na jam'iyyun adawa, Frank ya na ci gaba da kalubalantar shugaba Buhari dangane da wannan lamari na yanzu, inda ya hikaito yadda tsohuwar gwamnati ta Goodluck Jonathan ta gudanar da tafiye-tafiyen ta gauraye da gwamnoni da kuma sanatoci na jam'iyyar adawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel