Jawabin Kwankwaso yayin tabbatar da niyyar yin takarar Shugaban kasa

Jawabin Kwankwaso yayin tabbatar da niyyar yin takarar Shugaban kasa

Mun kawo maku abubuwan da tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Kwankwaso ya fada wajen taron kaddamar da shirin sa na takarar Shugaban kasa a zaben 2019. An yi taron ne jiya a cikin babban Birnin Tarayya Abuja.

Jawabin Kwankwaso yayin tabbatar da niyyar yin takarar Shugaban kasa
Tsohon Gwamna Kwakwaso yace Gwamnatin sa za ta hada-kan ‘Yan Najeriya
Asali: Twitter

1. Sukurkucewar abubuwa a kasa

Rabiu Kwankwaso ya nuna cewa asarar lokaci ne ma mutun yace abubuwa sun cabe a Najeriya. A dallin haka ne ‘Dan siyasar yake neman takara domin inganta rayuwar al’umma a Kasar da su ke cikin wani hali.

2. Sha’anin tsaron kasa

Sanata Rabiu Kwankwaso ya nuna cewa idan har ya samu mulki, zai yi kokari wajen ganin an daina amfani da Jami’an tsaro wajen cin ma burin siyasa tare da ba Sojojin Najeriya da ‘yan Sanda kayan aiki.

3. Tattalin arziki

Bayan nan kuma tsohon Gwamnan yayi alkawarin babbako da tattalin arzikin Najeriya. Kwankwaso ya koka game da yadda ake fama da tsadar kayan masarufi da rashin aikin yi da kuma wahalar kasuwanci.

KU KARANTA: Abin da Gwamnati na za tayi idan na dare mulki - Kwankwaso

4. Samawa jama’a aikin yi

Tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso wanda yake neman takarar Shugaban kasa a zaben 2019 ya sha alwashin ganin Talakawa sun samu hanyar cin abinci ta hanyar kawo tsare-tsaren da su agazawa ‘Yan kasuwa da masu sana’a.

5. Harkar man fetur

Haka zalika, ‘Dan takarar Shugaban Kasar na Jam’iyyar PDP yayi alkawarin cewa idan ya samu mulkin Najeriya, za a daina satar dukiyar kasa ta bangaren harkar man fetur tare da karkatar da akalar Gwamnati daga mai.

6. Habaka harkar ilmi

Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Rabiu Musa Kwankwaso yayi alkawarin inganta harkar ilmi a kasar nan idan har ya zama Shugaban Kasa a 2019 domin ganin an samu hadin kai da rashin banbanci tsakanin al’umma.

7. Hadin kan al’umma

Kwankwaso ya nuna cewa zai hada-kan al’ummar kasar nan idan ya samu mulki, A cewar sa, idan yayi mulki babu maganar wani Bahaushe, Bayarabe, ko Inyamuri sai dai ayi maganar zama cikakken ‘Dan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel