Zaben 2019: Dan Sarki zai fafata da gwamna mai a wata jiha a Arewa

Zaben 2019: Dan Sarki zai fafata da gwamna mai a wata jiha a Arewa

- Jahohi da dama zasu fuskanci zazzafar fafatawa yayin fitar da dan takarar gwamna

- Cikin irin wadannan jahohi har da jihar Kebbi

- Sai dai tun yanzu wanda ke shirin yin takarar da gwamna mai cin ya fara fuskantar kalubale

Alhaji Ibrahim Mera dan gidan tsohon Sarkin Argungun ya bayyana kudurinsa na yin takarar gwamnan jihar Kebbi a karkashin tutar jam’iyyar APC, a kakar zaben shekarar 2019.

Zaben 2019: Dan Sarki zai fafata da gwamna mai a wata jiha a Najeriya
Zaben 2019: Dan Sarki zai fafata da gwamna mai a wata jiha a Najeriya
Asali: Facebook

Ibrahim Mera wanda tsohon mukaddashin shugaban hukumar fasa kwauri ta kasa ne kuma dan uwa ga Sarkin Argungu mai ci Dakta Sama'ila Mera, ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a ofishin jam’iyyar APC dake birnin Kebbi.

Hakan na nufin Alh. Ibrahim Mera zai fafata da gwamna mai ci Dakta Atiku Bagudu a zaben fidda gwani na jam’iyyar ta APC.

Ibrahim Mera ya shaida cewa “Bukatar yin takara ta ta biyo bayan yadda dubban magoya baya da suka bukaci hakan da kuma kaunar cigaban jihata ta Kebbi".

KU KARANTA: Abin da zan yi idan na samu mulkin Shugaban kasa a 2019 - Kwankwaso

“Bayan kammala aikin da nayi cikin sadaukarwa da hazikanci, sai na yanke shawarar fitowa takara domin hidimtawa jihata, don bunkasa cigabanta".

Amma sai dai nasa bangaren sakataren kudi na jam’iyyar APC na jihar Kebbi Alhaji Bala Kangiwa ya ce tuni jam’iyyar APC ta tsayar da Atiku Bagudu a matsayin dan takarar gwamnan jihar ta Kebbi.

“A matsayinka na mamba a jam’iyyar APC, amma kuma tsahon shekaru uku ke nan dai-dai bamu ga idonka a dukkanin wani taro da jam’iyyar APC take yi ba, amma duk da haka kana ikon yin takarar kowanne mukami a cikin Jamiyyar APC" In Ji Bala Kangiwa ya bayyana.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel