2019: Atiku ya dauki wani alkawari yayin murnar tarbar da aka yi masa a jihar Neja, duba hotuna

2019: Atiku ya dauki wani alkawari yayin murnar tarbar da aka yi masa a jihar Neja, duba hotuna

- Ayarin neman yakin zaben tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya isa jihar Neja a cigaba da neman goyon bayan ‘yan jam’iyyar PDP

- Atiku, cikin murna da jin dadin karamcin da jama’a suka nuna masa, ya bayyana cewar ba zai kara ficewa daga jam’iyyar PDP ba

- A yau, Alhamis, ne shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana sha’awarsa ta shiga neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta PDP

A cigaba da tuntuba da neman goyon bayan ‘yan jam’iyyar PDP da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ke yi a fadin Najeriya, ayarin neman zaben nasa ya ziyarci garin Neja na jihar Minna.

2019: Atiku ya dauki wani alkawari yayin murnar tarbar da aka yi masa a jihar Neja, duba hotuna
Atiku a jihar Neja
Asali: Twitter

2019: Atiku ya dauki wani alkawari yayin murnar tarbar da aka yi masa a jihar Neja, duba hotuna
Atiku a jihar Neja
Asali: Twitter

A sakon da Atiku ya rubuta a shafinsa na Tuwita, ya nuna jin dadinsa bisa ganin yadda ‘ya’yan jam’iyyar PDP suka yi dandazo wurin fitowa domin tarbar sa. Jin dadin karamcin da ‘yan jam’iyyar suka nuna masa, Atiku ya shaida masu cewar ba zai kara fita daga PDP ba.

DUBA WANNAN: Wata masarauta a Zamfara zata fara yiwa kauyuka da rugar Fulani maja

Kazalika, Atiku, ya nuna karkasashinsa na lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP matukar za a bawa dukkan ‘yan takarar shugaban kasa dammar gwada farinjininsu.

Atiku ya yi kira ga shugabancin jam’iyyar PDP na kasa das u nuna dattako wajen gudanar da zaben adalci yayin fitar dad an takarar da zai wakilci jam’iyyar a zaben shekarar 2019.

2019: Atiku ya dauki wani alkawari yayin murnar tarbar da aka yi masa a jihar Neja, duba hotuna
Atiku a jihar Neja
Asali: Twitter

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel